✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ASUU ya isa haka nan

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta fara yajin aikin gargadi na mako biyu a ranar 9 ga watan nan da muke ciki domin tursasa Gwamnatin Tarayya…

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta fara yajin aikin gargadi na mako biyu a ranar 9 ga watan nan da muke ciki domin tursasa Gwamnatin Tarayya wajen aiwatar da yarjeniyoyin da suka cimma a bara. Da yake magana a Enugu bayan taron da Majalisar Zartarwar Kungiyar ta Kasa  ta gudanar a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu, Shugaban Kungiyar ASUU ta Kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce yajin aikin na da manufar tilasta gwamnati ta aiwatar da ragowar yarjeniyoyin da suka cimma da kungiyar a shekarar 2009 da 2013 da 2017 da kuma Yarjejeniyar Aiwatar da Aiki MoA a 2019.

Ogunyemi ya ce, “Bayan tattauna tanade-tanaden da suke cikin yarjejeniyar 2009 a tsakanin bangarorin biyu – ASUU da Gwamnatin Tarayyar – Yarjejeniyar Fahimtar Juna, MoU ta shekarar 2013 da kuma ta Aiwatarwa ta 2017, wadanda duk ba a aiwatar ba, Majalisar Zartarwar Kungiyar ta amince da shiga yajin aikin gargadi na mako biyu – da zai fara daga ranar 9 ga Maris 2020.” Ya kuma ce, ASUU za ta yi amfani da lokacin yajin aikin domin warware kiki-kakar da take tsakanin kungiyar da Gwamnatin Tarayyar kan batun tsarin nan na biyan albashi na IPPIS. Gwamnatin ta katse biyan ma’aikatan jami’o’in albashin watan Fabrairu wadanda suka ki shiga tsarin na IPPIS.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan taron da bangarorin biyu – gwamnati da ASUU – suka yi a ranar Alhamis din makon jiya – Ministan Kwadago da Ingancin  Aiki, Chris Ngige, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gindaya sharuddan shigar da jami’o’i a tsarin tabbatar da gaskiya da amana a harkokin gudanar da jami’o’in (UTAS) wanda Kungiyar ASUU take kokarin gabatar wa ga tsarin gwamnatin na IPPIS. Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da Ngige ya ayyana yajin aikin gargadin a zaman wanda ba ya da halacci. Sai dai kuma bangarorin biyu sun tsara sake zama a ranar 17 ga watan Maris 2020 domin ci gaba da musayar miyau. Ita ma Majalisar Wakilai ta tsoma baki cikin lamarin a ranar Alhamis din makon jiya.

Idan za a iya tunawa bayan da gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar a Nuwamban 2016 – ASUU ta shiga yajin aikin sai illa masha Allahu a ranar 4 ga Nuwamban 2018; amma ta dakatar da shi a ranar Alhamis 7 ga Fabrairun 2019 bayan an sake cimma sabuwar yarjejeniyar aiwatarwa da Gwamnatin Tarayya. Muhimman ababuwan da aka cimma a yarjejeniyar sun hada da: (1) Sake Naira biliyan 25 ga jami’o’in a watannin Afrilu/Mayu 2019 bayan nan kuma gwamnati za ta fara aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da aka cimma a 2013. (2) Biyan wani kaso daga kudaden ariyas na malaman. (3) Karfafa Kwamitin Tuntuba game da Jami’o’in Jihohi domin duba batutuwan gudanar da su da kuma rashin isassun kudi. (4) Tura kwamitocin ziyara ga dukkan jami’o’in Gwamnatin Tarayya da aka amince zai fara ranar 11 ga Maris 2019. (5) Bayar da lasisin fara aikin Kamfanin Kula da Fenshon Jami’o’in Najeriya, (NUPEMCO).

In ban da Kamfanin NUPEMCO wanda ya fara aiki, sauran batutuwan Yarjejeniyar Aiwatar da Aikin da Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu a kai, dukkansu ba ta martaba su ba. Tsayuwar gwamen jakin da gwamnatin ke yi a kullum wajen aiwatar da mafi yawan yarjeniyoyin da ta cimma da ASUU ne kusan dalilin shigar kungiyar yajin aiki kusan kowane lokaci. Ya kamata gwamnati ta fahimci cewa ta yi alkawarin aiwatar da yarjeniyoyin da ita kungiyar. Ita kuma ASUU ta fahimci cewa yawaitar shiga yajin aiki a kullum ba shi ne mafita ba. Yawaitar shiga yaje-yajen aiki ya sa kungiyar ta rasa goyon bayan jama’a koda kuwa akwai kwakkwaran dalilin shiga yajin aikin. Yajin aikin da suke a yanzu babu dalilin shigarsa, domini ta kungiyar ba ta yi amfani da wasu dabarun na daban wajen warware bakin zaren kamar farfagandar kafafen watsa labarai da matsin lamba kan Majalisar Dokoki ta Kasa da gudanar da zanga-zangar lumana tare da neman warware batun a Kotun Ma’aikata. Ta wadannan hanyoyi, ASUU za ta iya samun biyan bukata ba tare da ta dauki matakan rufe makarantu ba.

Daliban jami’o’in gwamnati da iyayensu ne kullum ke shiga tasku idan ASUU ta shiga yajin aiki. A wasu lokuta iyayen da ke hannu da shuni kan tura ’ya’yansu karatun digiri na farko kasashen ketare ba domin komai ba, sai don guje wa yawaitar yaje-yajen aiki a jami’o’in Najeriya. Lalacewar ingancin karatu daga daliban da suka gama jami’a a Najeriya ba ya rasa nasaba da irin shiga yajin aiki barkatai da ASUU ke yi. Yayin da muke kiran ASUU ta yi gaggawar janye yajin aikin, muna kuma kira ga gwamnati kanta ta aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da ta cimma da kungiyar.  Yaje-yajen aikin da kuma gazawar yarjeniyoyin sun isa haka nan.