✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da Boko Haram bai kare ba – Burutai

Babban Hafsan Sojin kasa Laftana Janar Tukur Burutai ya ce duk da cewa sojojin Najeriya sun karya lagon ’yan Boko Haram bayan sun samu nasarori…

Babban Hafsan Sojin kasa Laftana Janar Tukur Burutai ya ce duk da cewa sojojin Najeriya sun karya lagon ’yan Boko Haram bayan sun samu nasarori da dama a yakin da suke yi da mayakan kungiyar, har yanzu ba a kammala yakin ba, don haka akwai bukatar a kara kaimi don murkushe su baki daya.

Janar Burutai ya yi wadannan kalamai ne lokacin da yake jawabi a wajen bude taron bayar da horo ga sojoji karo na 19 a Bauchi, inda ya ce akwai bukatar a hana ’yan Boko Haram din sake taruwa ko samun damar da za su sake farfadowa su rika kai hare-hare.

Janar Burutai wanda Babban Jami’in Samar da Kayayyakin Ayyukan Soji, Manjo Janar Rogers Ibeh Nicholas ya wakilce shi, ya ce ya zama tilas a rika bai wa sojoji sababbin dabarun yaki na zamani domin su rika taka rawar da ta dace wajen kare kasa a kowane lokaci, wanda hakan ne dalilin kirkiro horaswa daban-daban ga sojojin kuma a kai-a-kai.

Taken taron na bana shi ne: “Yadda ya kamata a inganta damar da sojojin Najeriya ke da shi ta shawo kan ayyukan da suke barazana ga harkokin tsaro a wannan zamani.” Janar Buratai ya ce sojoji na bukatar a samar musu da kayayyakin aiki masu inganci, “Don haka za mu yi duk abin da za mu yi mu samar musu da duk kayayyakin yaki na zamani da suke bukata domin samar da kayayyakin aikin soji na zamani shi ma wani abu ne cikin dabarun yaki,” inji shi.

Sai ya ba sojojin tabbacin cewa hedkwatar tsaro za ta ci gaba da samar musu da kayayyakin aiki da kuma gyara matsugunansu da kyautata jin dadinsu.

Janar Burutai ya kuma tabbatar musu da cewa za a rika kula da makamansu da kuma saya musu manyan makamai da sauran kayayyakin aiki da suke bukata, kuma za a ba su cikakken horo. Ya ce bayan an gama wannan horo na mako guda za a kafa wani karamin kwamiti da zai kawo wani tsari da za a rika bi ana samar musu da makamai da kayayyakin aiki da yadda za a rika gyara da kula da makaman da kayayyakin aikin.

A jawabin mukaddashin Kwamandan Kula da Lafiyar Sojoji, Birgediya Janar Clifford Brown ya ce horarwar ta mako guda horo ne da ake yi shekara-shekara domin zaburar da sojojin da koya musu sababbin dabaru.