✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya: Nazari a Mahangar Musulunci

Wannan wata lacca ce da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani a taron lauyoyi…

Wannan wata lacca ce da Babban Lauya Ustaz Yusuf Alaoye Ali (SAN) ya gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani a taron lauyoyi Musulmi da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abekuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara ta kamar haka:

Gabatarwa:                                                                                                                                                                                                                                                                                                          Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ara mana rai har muka sake samun damar halartar wannan taro mai albarka na Hidimar Musulmi ga Shari’a da ake gudanarwa kowace shekara. Ina kuma mika godiyata ga wadanda suka shirya wannan taro, suka kuma gayyace ni don in gabatar da jawabi a kan wannan maudu’i: “Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya” don yin nazari a kan kalubalen da yakin ke fuskanta, ta mahangar addinin Musulunci. Muna rokon Allah Ya datar da mu kan abin da za mu tsinkayo a wannan tattaunawa.

Lallai babu shakka sanin kowa ne cewa yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, tun shekaru da dama da suka gabata, ya hadu da tasgaro da rikice-rikice da kalubale iri-iri. Wannan ya sa cin hanci da rashawa a Najeriya ya zamo tamkar cutar nan ta kansa (daji ko sankara) – duk ma’aikatun gwamnati da na masu zaman kansu, da ta bulla, to shi ke nan; wannan ma’aikatar ta gama rushewa! Ga shi kuma sai habaka take yi kamar wuter daji – ta ko’ina sai kunno kai take yi. Da haka, da haka sai da ta kai aka rasa kanta da tushenta; ballantana a san makamar magance ta. Shi ke nan sai ta kambama ta kuma fadada har ta kai matsayin bijire wa duk wani kokari na dakile ta.

Yanzu matakin da ake ciki shi ne, ta kai duk wanda yake so ya yi mu’amala da wata hukuma ta gwamnati ko mai zaman kanta, to sai ya fara tunanin mene ne hanci ko ‘na goro’ ko ‘alherin’ mahukuntan wannan hukuma tukuna. Kai ba ta tsaya iya nan ba, ko su a tsakaninsu, mahukuntan gwamnatin wajen a tabbatar ko a karbi wani aiki da suka aiwatar a gwamnatance, sai ka ga cin hanci yana gudana a tsakaninsu.

An lura cewa mafi yawan ’yan Najeriya, ’yan siyasa da ma’aikatan gwamnati wadanda suke cikin aiki da wadanda suka yi ritaya da alkalai, kai har ma da sojoji suna fadawa cikin wannan ta’ada ta cin hanci da rashawa. Kodayake an fi ganin ’yan siyasa su suka fi kowa hannu dumu-dumu cikin wannan ta’asar saboda kulafacinsu na son dafe madafun iko, sai ka ga sun bude kofar ya-ki-halal-ya-ki-haram don azurta kansu da kuma samun kudaden yin kamfen da yin magudin zabe. Wani lokacin ma za ka ga suna nuna cewa suna yin haka ne a madadin jam’iyyarsu da za su tsaya takara a cikinta amma fa a can kokuwar zuriyarsu, suna yin haka ne don azurta kansu kawai.

Cin hanci da rashawa, wanda ya hada da yin algushi wajen aikin gwamnati da yin almundahana da nuna son kai da kuma wawashe dukiyar mutane da jami’an gudanar da dukiyar suke yi, ya balbaltar da tsarin gudanar hukumomin gwamnati da ma na masu zaman kansu da kashi mai tarin yawa.

A Najeriya, ta kai matsayin da an daina tambayar wane ne mai cin hanci da rashawa (don kusan kowa yana yi), sai dai ka ji ana laluben su wane ne ba sa cin hanci da rashawa, (saboda karancinsu cikin al’umma). Haka abin yake idan aka yi la’akari da yadda ’yan Najeriya suka zama ’yan ya-ki-halal-ya-ki-haram don gudanar da rayuwa mai tsada da jajibo wa kansu rayuwar da ta keta ainihin samunsu.

Wani babban abin damuwa da tashin hankali shi ne, yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu cikin shugabannin addinai, wadanda a asali ya kamata su yi hannun-riga da wannan muguwar ta’ada, su kuma koya wa mabiyansu yadda za su zama masu gaskiya da rikon amana da kamewa daga barin haram da jin tsoron Allah cikin gudanar da al’amuransu. Amma sai ga shi da su ake gogayya wajen yin hafzi da ‘romon’ wannan mummunar ta’ada mai halakarwa.

Cin hanci da rashawa fa, Allah gafarta malam ya mamaye dukkan bangarori na rayuwar al’ummarmu, wadda hakan ba ya rasa alaka da tunanin nan da ’yan Najeriya suke da shi na cewa wai ba abin da zai gudana yadda ya kamata a hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu kuma a ci nasara, ba tare da an kai caffa ga wannan mummunar dabi’a ta cin hanci da rashawa ba.

Babu shakka, an yi amfani da hanyoyi iri daban-daban don kashewa ko dakile wannan wutar daji da ta dade tana ci ganga-ganga cikin al’ummar kasar nan amma ba tare da an kai ga cin ma nasara ba, ko ma akalla a rage karfin ruruwarta. Da haka ne, kullum wannan masifa sai kara ta’azzara da ban-tsoro da kashe gwiwar gwamnatoci daban-daban take yi, wadanda suka shude da kuma masu ci. Saboda haka, a wannan tattaunawa tamu, za mu yi duba na tsanaki ta mahangar Musulunci, don lalubo makaman yakar wannan mummunar ta’ada mai tabarbarar da al’umma. Za mu yi haka ne ta hanyar lizimta wa kanmu yin bayani kan yadda aka fahimci cin hanci da rashawa a al’adance da a hukumance da kuma a Musulunce, sannan mu yi izna da wasu tabbatattun mafita daga wannan annoba. Za mu yi haka ne, bayan mun zakulo dalilan da cin hanci da rashawa da mummunar tasirinta wajen rasa kasa, duk a Mahangar Musulunci. Daga karshe mu karkare da zayyano shawarwari wadanda idan aka yi amfani da su, to za a kai ga cin ma nasara cikin yaki da wannan annoba ta cin hanci da rashawa.

Shin mene ne cin hanci da rashawa?

Daidaikun mutane da masana daga fannoni daban-daban na rayuwa sun ba da ta’arifi gami da yin bayani ta fuskar fannin da suka lakanta a kan abin da ake nufi da cin hanci da rashawa. Dokoki a matakai na gwamnati daban-daban ba a bar su a baya ba wajen kalailaice abin da ake nufi da cin hanci da rashawa.

Ga misali, Farfesa Stephen D. Morris, Shehin Malami ne a fannin Kimiyyar Siyasa, ya rubuta cewa: “Cin hanci da rashawa a siyasance yana farawa ne daga rububin kai wa ga jibintar al’amuran mutane ta haramtacciyar hanya (magudin zabe da sauransu), don amfanin su masu gudanarwar da wasu ’yan tsiraru kawai.”

Shi kuwa masanin tattalin arziki, Ian Senior, cewa ya yi: “Duk wani abu (na goro, ko wata fa’ida) da wani zai bayar a asirce, don shi wannan (mai karbar ‘na goron’) ya zame wa wancan (mai ba da ‘na goron’) wani tsani don yin hafzi da wani abu wanda a zahiri (shi wancan mai ba da ‘na goron’) bai cancanci samun wannan abin ba, to shi ake nufi da cin hanci da rashawa.”

Daniel Kanfmann, wani jami’i ne na Bankin Duniya. Shi kuma ganowa ya yi ana iya shirya cin hanci da rashawa a cikin dokokin da ake yi don gudanar da gwamnati da jama’a. Hakan na faruwa ne ta yadda majibintar gudanar da sha’anin gwamnati kan kirkiri dokoki ko sarrafa wadanda ake da su, don yin daidai ko ba su kariya ga muradinsu na kaiwa ga gaci cikin aikata wannan mummunar ta’ada ta cin hanci da rashawa.

Za mu ci gaba