Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (4)

Yan sandan Najeriya a bakin aikin tabbatar da tsaro

Hanyar magance cin hanci da rashawa a mahangar Musulunci:

Musulunci shi ne addinin daya tilo da yake da ruwa-da-tsaki cikin gudanar da kacokan din rayuwar mabiyansa.  Don haka ne Musulunci ya yi umarni ga kowane Musulmi ya zama mutumin kirki, mai tsoron Allah wanda ya wofinta daga aikata munanan ayyuka, ya kuma damfaru da aikata kyawawa cikin al’amuransa dukansu.

ADVERTISEMENT

Kasancewarsu masu tsoron Allah, shi ne mataki na farko kuma cikamakin matakan maganin matsalolin da cin hanci da dan Adam zai tsinci kansa a yanzu da kuma nan gaba, a cikin rayuwarsa. Mafi girman daraja ga mutum Musulmi a cikin mu’amalarsa, shi ne ya zamo mai gaskiya da yin adalci da taimakon gajiyayyu da mabukata da girmama iyaye da na-gaba da malamai da kuma nuna jinkai ga mata da kananan yara da sauransu.

Musulunci bai tsaya nan ba, sai da ya haramta wa Musulmi yin yasasshiyar magana da kisan ran da ba bai ji ba, bai gani ba da yin ta’addanci da cin zali da rashin adalci da bakar gaba da zinace-zinace da shaye-shaye da dai sauransu.

ADVERTISEMENT

Wannan umarni da hani suna tabbatar da Musulunci shi ke rike da ragamar gudanar da rayuwar Musulmi kacokan dinta. Don haka ne Allah Mai girma da Daukaka Yake fada a cikin Alkur’ani, cewa: “Ka ce (Ya Annabi Muhammadu), lallai Sallata da yankana da rayuwata da mutuwata, (duk ina yin su ne) ga Allah Ubangijin talikai…”

Wannan aya tana nuna cewa duk abin da Musulmi zai yi, to yana yin sa ne gwargwadon tanade-tanaden da Musulunci ya yi. In kuwa haka ne, to ba wani abu a cikin Musulunci illa na umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna.

Nan baya kadan, mun ambaci dalilan da suke haddasa cin hanci da rashawa a cikin al’umma. To yanzu bari mu kutsa don gano yadda za a magance wannan annoba ta cin hanci da rashawa, ta yin la’akari da hanyoyin da Musulunci ya shimfida don samun gwamnati da al’umma irin wadda Allah da kanSa Ya yaba saboda umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna, in an bi su.

Allah Ya ce: “Ku (al’ummar Annabi Muhammadu) kun kasance mafi alherin al’ummai da Allah Ya taba halitta, (saboda) kuna umarni da kyakkyawa kuma kuna hani da mummuna; sannan kuna imani da Allah…” (Alkur’ani: 3:110).

Daga wannan aya ta sama, ya bayyana karara cewa shika-shikan kafuwar gwamnati ko al’aumma tagari su ne umarni da kyawawan ayyuka don dabbaka su da kuma hani da munana don nesantarsu, duk cikin yin imani da Allah Madaukaki. Wadannan ginshikai guda uku na samun al’umma tagari idan aka dasa su kuma aka bi su sau-da-kafa, to, babu shakka za su taimaka wajen yaka da kuma kakkabe cin hanci da rashawa a cikin al’ummarmu. Umarni da kyakkyawan aiki: Duk al’ummar da mafi yawanta ke umarni da aikata kyawawan ayyuka, to babu shakka za ta zama mai cike da salama da natsuwa a ban-kasa, tunda sakamakon mai aikata alheri shi ne samun alherin don aikata ayyuka na alherin. Kamar yadda Allah Mabuwayi Ya fada a cikin Alkur’ani (55:50), inda Yake cewa: “Mene ne sakamakon alheri in ban da (samun) alheri kwatankwacinsa?” Amma abin bakin ciki, mafi yawan ’yan Najeriya, aikata alheri ya yi gabas su kuma sun danna yamma a guje! Wannan ya sa muka tsinci kanmu cikin irin wannnan mummunan hali da muke ciki a halin yanzu. Ko shakka babu, cin hanci da rashawa da muke ta tafkawa ta fuskoki daban-daban a kasar nan, ba komai ne ya haddasa su ba illa rashin tarbiyyar umarni da dabbaka kyawawan ayyuka.

Musulunci yana kallon dabi’ar cin hanci da rashawa da suka yi katutu a tsakanin al’umma, a matsayin son kai da son tara abin duniya cikin dare daya, don haka ne Musulunci ya yi umarni da tsantseni da kamewa ta hanyar yin adalci da daidaita al’amura da yin gaskiya da jin tsoron Allah da nuna duk wani halin kirki. Allah Madaukakin Sarki Ya fada a cikin Alkur’ani (11:25) cewa: “Ya ku mutane! ku cika awo da mizani cikin adalci, sannan kada ku cuci mutane cikin kayansu, sannan kada ku aikata rashin adalci a bayan kasa kuna masu (haddasa) fasadi.”

Wannan aya tana nuna yadda Musulunci ya nuna balo-balo wajen kin duk wani nau’in ayyukan ki da suka hada da cin hanci da rashawa. Sannan, a dai ayar, ta yi kira da aikata duk wani halin kirki da ya hada da adalci a tsakanin mutane, duk saboda a samu  daidaito da girmama doka da zaman lafiya da karuwar arziki a tsakanin mutane. Da wannan ne za a iya fahimtar cewa, shi Musulunci kullum yana kira ne da kuma tabbatar da wani tsari ga duniya baki daya da zai inganta tsakanin mutane da Mahaliccinsu, da a tsakaninsu a karan kansu, kai har da tsakaninsu da sauran halittu (dabbobi da sauransu), ta hanyar yin adalci da daidaito a tsakanin mutane, wanda yin hakan ba kawai zai tabbatar da walwala a tsakanin mutane ba ne, a’a, har da samar da al’umma nagartacciya mai kuma gaskiya.

Gaba daya dai abin nufi a nan, a duk sa’ar da aka samu al’umma tana umarni da kuma aikata kyawawan ayyuka, to wannan al’ummar za ta yi baram-baram da cin hanci da rashawa da duk dangoginsu.

Hani da aikata mummunan aiki: Hani da aikata mummuna, babu ko shakka cikamakin tabbatuwar umarni da aikata kyakkyawan aiki ne, domin kuwa a duk sa’ar da mutane suka dukufa wajen aikata kyakkyawan aiki, to wannnan na nufin aikata mummuna aiki zai samu mummunar koma baya, in ma ba su yi adabo da shi ba. Ke nan duk inda ka ji umarni da aikata kyakkyawan aiki, to ka ji hani da mummunan aiki – Danjuma ne da Danjummai.

Duk mutumin da yake kokarin aikata kyakkyawan aiki kuma yake kokarin haramta wa kansa aikata mummunan aiki, to zai yi wuya ka same shi yana handame dukiyar da aka samar don gudanar da bukatun da suka shafi al’umma, ko ka same shi yana cusa kai cikin kowace irin almundahana. Ashe ke nan duk al’ummar da ta tsinci kanta tana aiwatarwa ko dabbaka wadannan ’yan tagwaye (umarni da aikata kyakkyawa da kuma hani da aikata mummuna), to babu shakka, babu ta yadda za a yi ta tsinci kanta tana aikata wannan mummunar ta’ada ta cin hanci da rashawa.

Rashin ’yan tagwayen nan cikin al’ummarmu shi ya sa muka tsinci kanmu cikin halin da muke ciki. Musulunci kwata-kwata ya tsani duk wani sabo da kuma tara dukiya ta hanyar da ba ta dace ba. Annabin Rahama (SAW) ya umarci Musulmi su yi nesa daga azurta kansu ta hanyar haram, inda aka rawaito shi yana cewa: “Duk tsokar (jiki) da ta ginu ta hanyar cin haram, to ba ta da makoma (a gobe Kiyama) face wuta.”

A wani Hadisin kuma, Annabi Muhammad (SAW) ya nuna bacin ransa ga wani mai kula da karba da tattara zakka da ya kawo zakkar da ya karbo ya kuma ware wasu kayan da mutanen suka ba shi kyauta, amma sai ya ce masa: “Wane hakki kake da shi har kake ware wasu kana cewa naka ne? Yanzu da ka zauna a gidan mahaifinka (ba mu sa ka aikin karbo zakkar ba), shin za ka samu wadannan da kake cewa naka ne?”

Nan take Annabi (SAW) ya umarce shi ya maido da abin da ya ware don ba hakkinsa ba ne. Wannan Hadisin na koya mana yin tsantseni da duk wani abin amfani da zai gifta ta ofishin da aka ba mu amanar gudanar da shi, ba kawai duk abin da ya zo mana ba mu rika kallonsa a matsayin “alherin ofis” ba. Kullum Musulunci yana koya wa mabiyansa yadda za su mallaki zukatansu ta hanyar gintse soye-soyen zukatansu da ba sa kan hanya madaidaiciya. Sannan Hadisin yana kira ga duk wani Musulmi da ya tarbiyyantu da yin adalci da siffantuwa da halaye nagari da yin hannun-riga da duk wani mummunan aiki, don tabbatar da ci gaba mai dorewa a karan kansa da kuma al’umma gaba daya.