✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya: Nazari a mahangar Musulunci (6)

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani inda Babban Lauya Ustaz Yusuf O. Ali (SAN) ya gabatar a…

Wannan lacca ce da aka gabatar a ranar 26-9-2016, don kara wa juna sani inda Babban Lauya Ustaz Yusuf O. Ali (SAN) ya gabatar a wani taro da ake shiryawa duk shekara mai taken ‘Muslim Legal Year Serbice’ a babban Masallacin Egba, Kobiti, Abekuta, Jihar Ogun. Barista M.B. Mahmoud Gama (08130969818) ne ya fassara:

Yin cikakken amfani da hukumomi masu yaki da cin hanci da rashawa: Kafa hukumomin nan masu yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati, (ICPC da EFCC) da kuma samar da Hukuma Kula da Da’ar Ma’aikata (Code of Conduct Bureau) da kuma Kotun Da’ar Ma’aikata (Code of Conduct Tribunal) ba karamin dora dan-ba ba ne wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Amma abin takaicin shi ne, duk da cewa wadannan hukumomi sun kai ga samun ’yan nasarori nan da can, abin da za a iya sadarwa kai-tsaye shi ne, wadancan hukumomi, a mafi yawan lokuta suna barin jaki ne suna dukan taiki! Haka ya faru ne saboda ’yan siyasa da suka kafa gwamnati suna mayar da irin wadannan hukumomi tamkar karnukan farautarsu wajen bata suna da daukar fansa kan abokan hamayyarsu ta siyasa.

Don haka akwai bukatar fadada aikace-aikace da hurumin da wadannan hukumomi suke da shi, game da ba su cikakkiyar damar gudanar da ayyukansu ba tare da nuna son kai ba. Dole wadanan hukumomi su rika gudanar da ayyukansu ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba.

Kara matsa kaimi wajen gano cin hanci da rashawa: Babu shakka, cikakken yaki da cin hanci da rashawa ba zai tabbata ba sai akalla an bi ta wadanan hanyoyi guda uku: (a) Dakile hanyoyin faruwar rashawar, (b) Ganowa da kuma (c) hukunta masu aikata ta. Zuwa yanzu dai ana dan kokari ta fuskar dakile ta (ta hanyar samar da dokoki da hukumomi amma ta fuskar kokarin ganowa da hukunta masu wannan mummunar ta’ada ta cin hanci da rashawa, abin yana nema ya gagari kundila. Saboda haka, yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na bukatar ba-sani-ba-sabo da kuma samun hukumomin da za su yi tsayuwar daka (irin wadda ’yan sanda ke nunawa a wajen shingayen tare motaci, ko irin wadda ’yan sandan-ciki ke nunawa wajen kare lafiyar Shugaban Kasa) wajen ganowa da hukunta ma’abota wannan mummunar ta’ada.

Fadada hanyoyin magance cin hanci da rashawa: Da za a dan daga kafa wajen kira da ake yi don rusa cin hanci da rashawa a Najeriya, to babu shakka da duk wata hada-hadar kasuwanci, da ta harkar ofis-ofis da ta zamantakewar mutane, ta zama ba abin da za ka iya gani da saurare ta ko’ina, in ba daidaitar al’amura ba. Wannan na alamta cewa, lallai-lallai akwai bukatar samar da sahihan shirye-shrye don ilimantarwa da wayar da kan mutane kan munanan illolin da cin hanci da rashawa ke haddasawa a Najeriya. Wannan  aiki ne da Hukumar Fadakarwa ta Kasa (NOA) da kuma Ma’aikatar Watsa Labarai ta Tarayya, ya kamata su tashi tsaye a kansa. Za su cimma nasarar wannan aiki ne idan suka yi amfani da shahararrun hanyoyin nan nasu na ilimantarwa da wayar da kan mutane. Wadannan hanyoyi su ne, rarraba wa mutane takardun da suke dauke da bayanan illolin cin hanci da rashawa (Hand bills),da lika manyan fastoci da ke dauke da bayanai a kan cin hanci da rashawa a wuraren taruwar jama’a (kamar tashoshin mota da kasuwanni, da sauransu) da yin amfani da jaridu da mujallu da sauran kafafen watsa labarai irin talabijin da rediyo da kafafen sadarwar zamani (Social Media), da sauransu. A lokaci guda kuma, a sanar da mutane ta wandanan kafofi, kan hukunce-hukunce masu tsauri da aka tanada ga duk wanda aka samu da hannu dumu-dumu cikin aikata wannan mummunar ta’ada.

Daga karshe a samar da wani tsari na shari’a wanda za a rika ganowa da gabatar da mai laifi a gaban kotu, don hukunta shi, cikin kankanen lokaci. Wadanan hanyoyi da muka zayyano a sama, na yi imani idan aka bi su sau-da-kafa, to za a cimma nasara, insha Allahu.

 

Mun kammala.