Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Yaki da Iran zai zama uwar dukkan yake-yaken da aka taba yi – Rouhani

Yaki da Iran zai zama uwar dukkan yake-yaken da aka taba yi – Rouhani

Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani ya ce kaki da kasar ka iya zama uwar kowane irin yaki da duniya ta fuskanta. An ruwaito Shugaba Hassan Rouhani yana fadin haka ne a wani jawabi da tashar talebijin din kasar ta watsa kai-tsaye a makon nan, yana  gargadin cewa zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar ruwan Hormouz na cikin hadari.

Zaman tankiya ta karu a tsakanin Iran da kasashen Yamma tun a bara, bayan da kasar Amurka ta sanar da ficewarta daga yarjejeniyar kasashen duniya da ta yi tanadin takaita shirin Iran din na bunkasa sinadarin Yuraniyum- domin a sassauta mata takunkumin tattalin arzikin da aka dora mata.

“Zaman lafiya da Iran, shi ne uwa ga kowane zaman lafiya; hakan nan ma yaki da Iran shi ne, uwar yaki ga kowane yaki.” Mista Rouhani ya furta haka ne a Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, ta cikin wani jawabi inda ya yi jinjina ga Ministan Harkokin Wajen Kasar, Mohammed Jabad Zarif; bayan da Amurka ta sanar da kakaba masa takunkumi a ranar 31 ga watan Yuli.

Idan har Amurka na son zama a teburin sulhu da Iran, to lallai ne Amurka ta janye dukkan takunkumin da ke kan Iran, inji Shugaba Rouhani, yana mai nanata cewa dole ne a kyale Iran ta fitar da manta zuwa kasuwannin duniya.

Wani abu da ake ganin ya kara rura wutar yiwuwar barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya, shi ne kame wani jirgin ruwan Birtaniya mai suna Stena Impero, a kusa da yankin mashigin ruwa na Hormouz a karshen watan Yuli da dakarun juyin juya-hali na Iran suka yi, bisa abin da suka kira keta dokokin sufurin ruwa da jirgin ya yi. Hakan ya zo ne mako biyu bayan da sojin ruwan Birtaniya suka kwace wani jirgin ruwan dakon mai kusa da yankin Gibraltar, kan zargin take ka’idar takunkumin da a a sanya wa Siriya.

“Mashigin ruwa domin mashigin ruwa ne. Ba zai yiwu a ce wai mashigin ruwan Hormuz, naku ne za ku iya watayawa a ciki; mu kuma a ce wai ba za mu iya watayawa a yankin mashigin ruwa na Gibraltar ba,” inji Rouhani.

An dai kiyasta kashi daya cikin biyar na man da ake hada-hada da shi a duniya, na shigewa ne ta mashigin ruwa na Hormuz.

Kafar labarai ta gwamnatin Iran, ta bayar da rahoton cewa askarawan juyin juya-halin kasar sun kwace wani jirgin ruwan dakon mai a yankin ruwa na Tekun Pasha a makon jiya, wanda suka ce yana fasakwaurin mai ne, sun kuma kama tare da tsare matukan jirgin su bakwai.