Search
Subscribe
Yaki ne ke neman barkewa a Kogi ba zaben Gwamna ba – Zarah Audu

Gimbiya Zahrah Mustapha Audu

Yaki ne ke neman barkewa a Kogi ba zaben Gwamna ba – Zarah Audu

Uwargidar wanda ya nemi tsayawa takarar Gwamna a APC a Jihar Kogi, Gimbiya Zahrah Mustapha Audu, ta yi zargin cewa ’yan takarar Gwamna a zaben 16 ga Nuwamba a jihar na shirn yaKi ne ba zabe ba. Gimbya Zahrah Audu ta yi zargin cewa akwai wani lamari da ke gudana na shigo da makamai gabanin zaben, kamar yadda ta shaida wa Aminiya.

Ta ce,  “Dukkanin ’yan takarar da ke neman kujerar Gwamnan Kogi na nuna alamun cewa sun shirya yin yaki ne fiye da yakin neman zabe. Idan kana yakin neman zabe don jagorantar al’umma, za ka fita ne kana jan hankalin masu kada kuri’a, ka lallashe su, sannan ka fada musu tanadin da ka yi musu, amma su ’yan takararmu na sayen motoci masu sulke da duk wani makami da alburusai.”

Zarah Mustapha ta yi kira ga Jam’iyyar APC da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan su shiga lamarin don ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin