✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yamadidin yaukaka yayyafin yarfe (1)

Girke-girke ne Sanwa suna ne Rabashen ragadada kowane Rubdugun rudi kankane Dandanon difarar dadi wanne ne   Kar ai yamadidin  ce-ce-ku-ce Dodorido yai fice Wajen…

Girke-girke ne

Sanwa suna ne

Rabashen ragadada kowane

Rubdugun rudi kankane

Dandanon difarar dadi wanne ne

 

Kar ai yamadidin  ce-ce-ku-ce

Dodorido yai fice

Wajen kirkira zance

Ko zaman zugar zauren zaurance

Dodo ne dai mai kwatance

 

A dai kaifafa zukatan tunani

Abin da ya kamata ai tuntuni

Kar a tsahirta wa malami masani

Gannan na-mujiya na iya gani

Batun ci-makar ciyayyar cin makani

 

An yi ikrarin rahusa

A dai hura a busa

Ka da tausar bodari ta turo tusa

A dan taushe da tausa

Kar a nuna gajiyawa a kasa

 

Yayyafi

Yafen yarfen yafi

Yaukaka yunkurin yaren yarfi

Yamadidin maganganun rufi

Yari-yarin yadiyar tsinin tsafi

 

’Yar tsala

Tsilla tsillar tsallen tsula

Tsinken tsallen tsagwaron tsunkula

Tsakure-tsakuren tsaron tsadar tsawwala

Tsammanin tsomomuwar tsimin tsumulmula

 

Tsautsayin tsimin tsiwar tsiya-tsiya

Ya damu da gaya

Kokon kunun tsamiya

Tumbatsar tukawar tumbin Tambaya

Turnukun tafarfasasshen hatsin hadidiya

 

Dambun dungun dambacewar damatsa

Tubanin tunkudo tumbin tumbatsa

Waskon wasa-wasar wartsakewa watsa-watsa

Gingimemiyar gurasar gutsira gatsa-gatsa

Lamurjen lemun lamusar lotsin latsin lotsa

 

Dabge

Da dage-dage

Duddugar duga-dugi doge

Durar dirkaniyar dibge

Dandanon dige-dige

 

Danwake da mai da yaji

Maganin mai rangaji

Gumurzun gwaramar Gogaji

Wadakar wargje wujijjigar Wargaji

Karime-karimen kamun kaji

 

An dai yi kalaci

An samu abin ci

Abin sha ba kunci

Tsawwalar tsada ba sassauci

Tsaka-tsakin tsakurar tsokaci

 

Talalar talauci

Tulin takaici

Dandani haukaci

Dari-darin hukunci

Haba-haban habaici

 

Kamun ludayi

Katantawar laulayi

Kiren kirgin kaikayi

Janjamin juriyar jama’ar juyi

Bangaje-bangajen bugun bayi

 

Yaushe za a daina kidahumanci

A zo ai adalci

A kawar da jahilci

A daina nuna bambanci

A mutunta kowa da mutunci

 

Kurungun matsala ya kunno

Ka’idar Karin kumallo

A samu koko da gayan kwallo

‘yar marar tuwo a mulmulo

Da rana a kwankwadi fura da nono

 

Yayimen-yayimen yaukaka yamadidi

Rangajin rumurmutsar ridi

Bikin bararrajewar barbadi

Camamar cinikin cukudi-cukudi

ci-makar cinkon cabin cin kudi

 

cabin cude-cuden cudi

rarume-rarumen rudi

raurawar rurin rade-radin radi

kwat-kwat kwankwadar na-kwadi

mahukunta a sammana sudi

 

mai kalangu yai kidi

mawaki mai yawan kaudi

sankira kirarinsa yai dadi

ba tsula madi

yadon yadiyar yadi

 

Bari batun bana balle badi

’Yan lalle na ta tadi

Adon-gari na zakwadi

Tsohuwa dai ta iya kadi

Tsokacinta shi ag gargadi

 

Sangarcewar sufurin safarar samfarera

Shasshekar sheke shanshera

Shuke-shuken shekara

Shashancin shantakewar shakara

Sunkurun sakarcin sake shawara

 

Tattagar tawagar Tayar-Landan

Kwashe-kwashen kayan Lantsandan

Ana ta budun-budun

Tulin tantakwashi na nan

Ko kun cinye saura kadan

 

Burgar bankar buskin-mati

Tulin taliyar tanti

Makaronin kanti

Kayan dadi a faranti

An jera ana ta fareti

 

Farfesun faskarar fakarar fama

Fargabar fahimtar fankama

Furkaniyar faskar farankama

Fama-faman fagamniyar fangima

Falle fuka-fukin filfilon fantama

 

Rani da damina

Harkar hatsi ake magana

Ina mai gayauna

Yaushe kake gyara gona

Kawai ka shantake ka zauna

 

Kayan dundume kururu na hauhawa

Da farshin kaya  ake kokowa

Motsin mutsttsukar matsolon motsuwa

Yankwane-yankwanen yunwa

Yarfen yaren yanyawa

 

Kantin kayan kwalama

Makwalashen moriyar manema

Mutane masu makama

Hakin hakilon hazartan himma

Batun burungujin burgamen birgima

 

Tereren takaddama

Tinkahon takun takama

Tinjimin tunbatsar tama

Takurar tunzura tuma

Tababar tantama

 

Kintacen kasassaba

Karambanin kwaba

Jigari-jigarin jibgin jiba

Soki-burutsun saba

Salon sabulun sassaba

 

Nomau na-manomi

Ka rike mukami

Kana kokarin motsa mukamuki

Kar ka haifar mana tarnaki

A kasa a zo ana jimami

 

Ka daina kimanta kudin koto

Hauro kofar hanci da zagaye

Za su ciyar da gari ya waye

Kafin hantsi yai kaye

A karke da cinikin toto

 

Mai dangauda da tubani

Kina ta yi iyaye da kakanni

Yanke miki ciniki ba tunani

Ki ta cura babba da kankani

Saye da sayarwa ba wuni-wuni

 

Manya ban da bambami

Ko mayen barasar mukami

Ai ta kwada wa jama’a sungumi

Ga damuwar dundumi

A wajen babba da karami

 

An dai haifar da jimurda

Mutane na rade-radin rada

An maishe da batu gada

Kowane sako batu ya sadada

Ana shan suburbuda

 

A kara yi wa mai gayauna agaji

Kar a ce an gaji

Ai yunkuri fardar daji

Ai ta himar kiwon kaji

A yi da karfin tada kwanji

 

A samar da taki

Yawansa ya zarta cikin taiki

Ya fi karfin dakon jaki

Ai zubi shukar ban mamaki

Mamakon yabanya ne batun baki

 

Karsana da nagge

Nono a nannage

Manshanu ba kage

Fadin fata ya fi karfin lage

Ai nashe-nashe bakuna a wage

 

Ba batun kage

Babu kwange

Ko kure kiren kanzon kurege

Ko artabun bera da mage

Sha’ani ne na hange-hange

 

Ciyayyar cin cukubus

Kalacin Karin kumallon kicibis

Aiken amsar alkubus

Barbaden garin bududus

Kwaramniyar kwasar kuskus

 

Garin kwaki a huta

Curin mandako ba karanta

Kwadon zogale kar a manta

Rama hana ramar mai mata

Rumurmutsar rummace na kwadaita

 

Tattasai da tumatur

’Ya’yan itacen fasa-dabur

Torokon tinkahon Tukur

Bambamim burka babur

A filin ta-mola a hura usur

 

A samar da naman bisashe

Mu ci mui lashe-lashe

Bakuna sui nashe-nashe

Mu koshi mu bar kwashe-kwashe

Fuskokinmu su washe

 

Mai tsiren  duniya

Dakon dakon dukiya

Damarar daukar dawainiya

Karajin kullin kugin kugiya

Ruftawar rufin rijiya

 

Manyan maciya

Malmalar marar tuwon toliya

Murjin mukekiyar muciya

Mamakon masakin makauniya

Makarar makoshin miskiniya

 

Manya ai furucin ingarma

Batu mai makama

Komai ya samu tushen zama

Ban da rangajin rungumar rigima

A dai kyautata rikon ragama

 

Jama’a na cin kwadon rogo

Wasu na gararamba da dankoko

Cikinsu har da mai makoko

Akwai masu fama da mashako

Ga shi an aiko muku sako

 

Ku kuwa kun make a fako

Mutane na son su leko

Ku dan yi musu wani abu a jinko

Ku kyautata halin riko

Sai ku hana mabukata roko

 

Girma-girma a kwatanta

Ai hankali a kimanta

Kar a maishemu malalata

Akwai dimbin  matalauta

Taimakon jama’a sai a daidaita

 

Bar batun wane ya ji ga wane

Ko dan wanene

Mu mike ka da mui zaune

Da na-mujiyarmu a kanne

Kowace harka mui kane-kane

 

A kauce wa dabarbarun ’yan sane

Masu tono binne-binne

Lamarinsu sananne ne

Don sukan haifar da zubar jinane

A karke da hande on bone

 

A daina terere

A zo ai kere-kere

Garmar gararumar gare-gare

Gundumar gungurawar gangare

Gunjin gwajajabar gyare-gyare

 

Abincin acici a arha

Rangwamen rahusa

Tumbin tukkuicin tusa

Tallace-tallacen tasa

Masu ciyayya sui masalaha

 

A fitar da kudin ciyar da jama’a

Tabahuwa a ce mata a’a

Kada kugin ciki ya zama kira’a

Lallai an taki sa’a

Don batun babu ba’a

 

An dai yi faman fatara

Karkara ana kakarar kara

Birane an rage tabara

Mahunkuntan nisan kin jin kira

Shi ya sa tallafi ya faskara

 

’Yan uwa ka da a kagara

A yi ta juriyar jira

Mahukunta ka da a makara

A daina kwado da dara

Sai al’umma ta sarara

 

Mun dai samu rahoto

An bude katafaren gidan koto

Ana hada-hada loto-loto

Dimbin jama’a can aka karkato

’yan dugwi-dugwi har da katoto

 

Ahir dinku masu neman na-bagas

Da masu cin bulus

Sai an lallaga muku jikkuna lilis

Ku dai kiyayi aikin ibilis

Ku fito da mtsabbai  ban da kus-kus

 

Sai a samu na cin algaragis

Kar a ruguzo rigis

A dai samu karfin takun tinkis-tinkis

A fafata da tabahuwa ai ragas

Cin modar gasa ko ai canjaras!