Da Dumi Dumi

‘Yan Afrika ta Kudu sun yi zanga-zangar kyamar baki

A yayin da jami’an tsaro suka kame wasu da dama bayan wata zanga-zangar kin jinin baki da al’ummar kasar Afrika ta Kudu ke yi wasu matasa dauke da muggan makamai sun gudanar  da zanga-zanga a yammacin jiya Lahadi, inda su ke neman lallai baki su gaggauta barin kasar.

Wani dan siyasar Afrika ta Kudu Mangosuthu Buthelez, da ya yi kokarin wayar da kan jama’ar kasar kan daina kyamatar baki, matasan sun tarwatsa taron.

Wasu kafofin yada labarai a kasar sun bayyana yadda aka fuskanci arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an ‘yan sanda lokacin da suka rika kone shaguna da kadarorin baki a birnin Johammesburg na kasar.

A cewar David Tambe shugaban ‘yan sandan kasar ta Afrika ta Kudu da ya ke tabbatar da lamarin, ya ce mutum biyu sun mutu sakamakon harbin bindiga da sukar wuka ko da dai bai bayar da tabbacin baki ne ko ‘yan kasar ne suka rasa rayukansu a hargitsin ba. Kamar yadda majiyar rfi Faransa ta ruwaito.

ADVERTISEMENT
Share