✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan aji dayan sakandare a Kano za su koma makaranta ran Litinin

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dukkanin daliban aji daya na babba da karamar sakandare su kamo makaranta daga ranar Litinin. Kwamishinan Ilimin jihar,…

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dukkanin daliban aji daya na babba da karamar sakandare su kamo makaranta daga ranar Litinin.

Kwamishinan Ilimin jihar, Muhammad Sanusi Kiru ya ce umarnain ya shafi daliban makarantun gwamnati da masu zaman kansu.

Sanarwar da Kakakin ma’aikatar, Aliyu Yusuf, ya fitar ta ce daliban makarantun kwana za su koma makaranta ranar Lahadi 15 ga Nuwamba, 2020 domin ci gaba da karatu ranar Litin 16 ga wata.

Ma’aikatar ta ce a ranar Litinin ta sama kuma daukacin ’yan firamare za su koma makaranta sabanin ranar da aka sanar da farko.

Ta bukaci da iyaye da masu kula da yara su lura da sabbin ranakun komawa makarantar shugabannin makarantu kuma su yi shirin karbar dalibai a kan kari.

Gwamnatin jihar ta umarci daliban aji daya na babba da karamar sakandare da su zauna a gida na tsawon mako biyar ne domin ’yan ajujuwan fita su kammala jarabawa.

An dauki matakin ne da nufin a rage yiwuwar yaduwar cutar COVID-19 wadda bullarta ta tilasta rufe makarantu da sauran tarukan jama’a a Najeriya da ma fadin duniya.