’Yan APC su yi taka-tsantsan wajen zaben shugabannin majalisa

Alhaji Umaru Maizabura

Shugaban Jam’iyyar NDLP, ta Kasa Alhaji Umaru Muhammad Maizabura ya shawarci ’ya’yan Jam’iyyar APC su yi taka- tsantsan wajen zaben shugabannin da za su jagorance su kada su sake kwata irin abin da ya faru a baya inda jam’iyyar adawa ta yi musu kutse a harkokin majalisar.

Bayan da Jam’iyyar APC ta yanke shawara kan wadanda za su jagoranci Majalisar Dattawa da ta Wakilai ne mutane suke ta fadin albarkacin bakinsu gudun kada a sake kwata ’yar gidan jiya, inda wadansu ’ya’yan Jam’iyyar APC suka hada kai da na Jam’iyyar PDP suka samar da jagororin majalisun biyu ciki har da na Jam’iyyar PDP abin da ya haifar da tafiyar hawainiya ga gwamnatin APC.

Alhaji Umar Maizabura, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Maiduguri, inda ya ce “Idan ’ya’yan Jam’iyyar APC suka yi sake irin na wancan lokaci to za a sake yi musu sakiyar da ba ruwa. Na lura a cikinsu akwai wadanda ba sa son ci gaban kasar nan, wanda hakan ya sa idan Shugaba Buhari ya mika musu wata bukata don ci gaban al’umman Najeriya, sai a ga sun yi kememe sun ki, to ka ga wannan sake ne daga ’ya’yan Jam’iyyar APC tun daga farko, domin akwai ayyuka da yawan gaske da muke bukata Shugaba Buhari ya aiwatar da su domin ci gaban kasa, amma ba su yiwu ba, saboda ’yan majalisar sun sa kafa su ture ana ji ana gani,” inji shi.

Ya kara da cewa “Don haka ina ba su shawara cewa su yi kokari su hada kansu su fid da mutumin da za a amince masa. Koda ba shugabannin Jam’iyyar APC ne suka fitar da jagororin ba, ya kamata a ce ’ya’yan jam’iyyar su amince da shawarar da aka yanke, idan kuma suna ganin bin hanyar zabe ce mafita, to ya kamata su yi kokari su hada kansu su fitar da mutum daya. Su tuna sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga, don haka ina kira su hada kansu su zama masu magana da  murya daya.’’

Da ya juya ga jam’iyyarsa ta NDLP kuwa, Shugaba Maizabura, ya jaddada cikakken goyon bayan jam’iyyar ga Shugaba Buhari, inda ya ce “Dama saboda kyawawan manufofin Shugaba Buhari na ci gaban al’umman kasar nan musanmman shirin yaki da cin hanci da rashawa da samar wa  matasa aikin yi ta hanyar N-Power, don ’ya’yan talakawa su samu aiki da farfado da tattalin arziki da inganta harkar tsaro, ya sa muke goyon bayansa.”

ADVERTISEMENT

Ya ce duk da cewa har yanzu akwai matsalolin tsaro a  Arewa, bai kamata a ce Shugaba Buhari ya gaza a harkar tsaro ba, domin masu garkuwa da mutane kamar ’yan yakin sunkuru ne ba a iya ganinsu. “Kai a wani lokaci ma za a iya kiransu da Boko Haram, saboda halayensu irin nasu ne, kuma sanin kowane barna lokaci daya ake yi, amma gyara sai a hankali, don haka wajibi ne a taimaki kasar nan da addu’a da fatan Allah Ya kawo mana karshen wannan sharrin. Kuma Shugaba Buhari a taimake shi da addu’a don ya samu krfin gwiwar yi mana aiki yadda kasa za ta zauna lafiya a  samu ci gaba,” inji shi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya