Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan Arewa mu hada kanmu

Haƙiƙa duk wata al’umma a duniya tana samun cikakken ci gaba ne ta fuskar haɗin kai da kaunar juna, tare da cire bambance-bambancen kabila ko addini ko yare. Wannan ne babban matakin kaiwa ga kowace irin nasarar rayuwa da samun dukkan ci gaban da ake buƙata.

Tun lokacin da Najeriya ta zama ƙasa mai cin gashin kanta, yankin Arewa ya taso da manyan mutane ’yan gwaggwarmayar ganin yankin ya samu duk wani ci gaba don ganin ya zarce tsara. Allah Ya jiƙan mazan jiya su Sardauna Gamji Dan Kwarai irin albarka da Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, tabbas waɗannan bayin Allah duk mai bibiyar tarihinsu ya san cewa sun ba da dukkan gudunmawa don ganin ci gaban Arewa. Duk mai bibiyar tarihin waɗannan bayin Allah ya san sun yi wa ƙasa hidima ta fuskoki da dama, sun bayar da lokacinsu, da dukiyarsu da rayuwarsu don ganin yankin Arewa ya zama mai faɗa-a-ji, kuma mai cikakken iko a  Najeriya.

ADVERTISEMENT

Idan da a ce waɗannan bayin Allah suna raye, to ko baƙin cikin irin halin da Arewa ta faɗa yana iya gamawa da su. Saboda faɗawar yankin a hannun marasa kishinta, masu son azurta kansu da iyalansu da ’yan uwansu.

Rashin haɗin kanmu shi ne babban jigon yin ƙafar ungulu ga duk wani shiri da aka yunƙuro za a yi wa wannan yankin domin samun maslaha, zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.

ADVERTISEMENT

Gamu da manyan mutane masu manyan muƙamai amma sun zama manyan  wofi, domin babu wani abin ci gaba da suke yi wa Arewar sai neman a haɗa kai da su a zalunci al’ummar yankin don kawai neman tara dukiya ko ta halin ƙaƙa.

Duk wani ɗan ƙasa nagari mai son ci gaban ƙasar, yana fafutikar kawo wani babban abin ci gaba wanda al’ummarsa za su yi alfahari da shi, kuma su yi masa addu’a a duk lokacin da suka tuna da shi, ko bayan wafatinsa.

Idan muka yi la’akari da waɗannan bayin Allah waɗanda na ambata tun farko, ai ba ƙuɗi suka bai wa al’umma ba, a’a. Sun yi wa al’umma aiki ne wanda ga shi har gobe ana tunawa da su, kuma ana gode musu akan gwaggwarmayar da suka yi ga jama’arsu, kasancewar ba su nuna bambancin ƙabila, ko yare, ko jinsi ba.

Wajibi ne gwamnonin Arewa da manyan mutane masu riƙe da manyan muƙamai a Arewa su haɗa kansu don kawo ci gaba mai amfani ga al’umma. Wajibi ne kowane mutum mai riƙe da wata kujera ya yi hidima ga al’ummarsa, saboda al’ummar su suka nuna bukatar ra’ayinsa kafin kaiwa ga wannan mukami da yake tinkaho da shi.

Shin Ruga da wadansu ’yan Kudu suke adawa da shi, sun samu kafar yin haka ne, saboda rikon sakainar kashin da wadansu daga cikin ’yan Arewa ke yi ne ga yankinsu, domin wadansunsu ma suna adawa da shi. Wani babban abin takaici ne yin sako-sako da wannan shiri, domin shirin zai taimaka matuƙa wajen ganin an magance rikice-rikicen manoma da makiyaya da suke laƙume dubban rayuka, inda wadansu suke yi amfani da damar da suka samu su mayar da abin ta’addanci a cikin ƙasa.

Babu shakka tun kafin zuwan Turawa ƙasar Hausa,  Hausawa da Fulani ’yan uwan juna ne, suna zaune lafiya da junansu, suna auratayya da juna suna komai tare. Sannan wuraren kiwo da ake cewa burtani kowace jiha daga cikin jihohin Najeriya tana da su, kuma filayen kiwon da ake kira da burtali yalwatattu ne, wanda hakan ya sa Fulani ba su kaiwa ga gonakin manoma su yi musu ɓarna wadda take jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin manoman da abokansu makiyaya.

A lokacin da muka ji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ambaci dawo da waɗannan wuraren kiwo ga makiyaya, mun ji matukar daɗi, kuma mun yi sam barka da haka. Amma babban abin takaici da Allah wadai shi ne a lokaci guda muka ji an dakatar da shirin saboda wata manufa ta siyasa, kuma haka sam ba daidai ba ne.

Yin adalci a tsakanin al’umma wajibi ne ba tare da nuna wariya ko bambanci ba, kamar yadda shi Shugaban Kasa ya dauki alƙawari lokacin rantsuwar kama aikinsa, kuma yake a rubuce a kundin tsarin mulkin ƙasar nan. Sannan wannan adalci yana da kyau a samar da shi ga kowa, hakan zai sa a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Duk da haka mun yi maraba da farin ciki da wasu daga cikin gwamnoninmu na Arewa da suka sha alwashin aiwatar da shirin. Arewa ce tamu, muna fata gwamnonin Arewa za su tsaya kyam don ganin shirin ya kankama, kuma ya yi tasiri. Babban burinmu shi ne mu ga kowa-da-kowa yana cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yana da kyau shugabannin Arewa su sanya kishin ƙasa gabansu fiye da buƙatun kansu, hakan zai taimaka wajen farfadowar Arewa da ƙimarta a idon duniya. Muna fatar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da lumana a ƙasarmu Najeriya da yankin Arewa baki daya.

Wassalam

Nura Muhammad Mai Apple, Gusau.