✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan banga sun harbe matashi a kan aski a Bauchi

A farkon makon nan ne wani abin takaici ya faru, inda ’yan sintiri da ake zargin na Kungiyar Garu Security ne suka harbe wani matashi mai…

A farkon makon nan ne wani abin takaici ya faru, inda ’yan sintiri da ake zargin na Kungiyar Garu Security ne suka harbe wani matashi mai suna Abubakar Mahmud, wanda aka fi sani da Abbati.

Aminiya ta samu bayanin cewa bayan matashin, ’yan sintirin sun kuma ji wa mutum hudu rauni, inda harsashinsu ya huda kwaurin wani, kuma sun sari wani suka cire masa yatsa, yayin da wata mata kuma suka ji mata ciwo har sai da aka yi mata dinki.

Da yake zantawa da Aminiya, dan uwan mamacin wanda ya ce yana wajen da abin ya faru, mai suna Yahuza Alhaji Shehu, wanda aka fi sani da Abu Ashraf ya ce: “A ranar Lahadin da ta gabata ’yan sintirin sun shiga Unguwar Ibo Kwatas a garin Bauchi da misalin karfe 8:00 na dare, ina gidan kawuna Magayakin Ajiyan Bauchi, suka same mu a zaune suka ce sun zo yi wa Mubarak ne aski. Sai suka cire masa hula suka ga babu gashi a kansa, suka wuce suka tafi. Can sai suka dawo a kungiyar fiye da mutum 20, suna zage-zage cewa dazu sun ga kamar ana yi musu guna-guni da kallon banza. Sai suka fara dukanmu da sanduna,” inji shi.

Ya kara da cewa “Sai marigayi Abbati ya ji hayaniya ta yi yawa ya fito ya tura sauran ’ya’yan Magayakin Ajiyan zuwa cikin shagonsa don kada a yi fada. Sai wani dan banga mai suna Lamaran, ya je jikin tagar shagon ya bankare, ya sa bakin bindigarsa ya saki harbi. Harsasan boris 28 suka samu Mubarak a ciki da kirji da mara da cinyarsa. Mutum takwas suke cikin shagon, kofa na kulle. Dan boris daya  ya samu wani mai suna Aliyu, ma’aikacin gidan burodi ya fasa masa kafa. Hakan bai yi musu ba, suka sari wani a hannu, suka yanke masa yatsa.”

Yahuza ya ce bayan sun tafi suka dauki Abbati suka kai shi asibiti, likita ya ce ya rasu kuma an ciro waharsasan boris din ga kuma bayanin da likitocin suka bayar da ya tabbatar da mutuwarsa.

“Sai muka dawo da shi gida, washegari Litinin muka yi masa jana’iza. Yaro ne mai hankali kuma jagora, mai taimakon kannensa da kokarin taimakon iyayens,” inji shi.

Ubangidan mamacin, Alhaji Yahaya Magayakin Ajiyan Bauchi ya ce baya nan lokacin da abin ya faru amma abin da ya tarar da abin da ya gani ya saba wa hankali.

“’Yan sintirin sun zo ne suka ce za su yi bincike, sai wanda aka kashen ya ce tunda bincike ne su tsaya su caje su, suka caje su ba su same su da wani abu na laifi ba,” inji Alhaji Yahaya.

Ya ce sun kira ’yan sanda, suka zo kuma aka tafi da ’yan sintirin zuwa caji ofis na cikin gari. Mutum shida aka kama aka ce an saki uku kuma an ce za a sake sakin guda biyu.“Gaskiya ba mu ji dadin sakinsu da aka yi ba kuma duk inda za mu je domin a bi mana hakkin wannan yaro nawa da aka kashe sai mun je, ba za mu bari ba. Ka samu mutum a wajen sana’arsa ka kashe shi, me ya yi maka? Ba za mu yarda ba,” inji shi.

Kakan Abbati mai suna Alhaji Ali Ahmed Danmasanin Ajiya, ya ce ya ji labarin kashe yaron ne kamar mafarki, musamman ganin matashin ya shirya ya fita zuwa inda suke aikin dinkin rigunan ’yan wasa na Magayakin Ajiya. Ya ja hankalin gwamnati ta soke lasisin irin wadannan kungiyoyi idan aka same su da laifi, saboda ba za su yi abin da ’yan sanda ke yi ba wajen tsare mutane. “Idan kuma ba haka ba za a wayi gari mutane su rika neman kare kansu daga ta’addancin irin wadannan kungiyoyi da suke daukar kananan yara ’yan shaye-shaye suna ba su bindiga da nufin su yi aikin samar da tsaro,” inji shi.

Mahaifiyar marigayin mai suna Hauwa Aliyu Ahmed, ta bayyana rashin jin dadin kashe danta, wanda ta bayyana cewa shi kadai ke tallafa mata wajen daukar dawainiyar iyayensa da kannensa da ke makaranta da wannan sana’a ta dinki da yake yi. Don haka ta roki gwamnati kan ta bi mata hakki wajen hukunta mutanen da suka kashe mata da kuma ta roki Allah Ya saka mata.

Shugaban Kungiyar ’Yan Sintiri ta Garu a Jihar Bauchi, Aliyu Ibrahim Yariman Dumi ya ce wannan mummunan aiki ya auku ne a lokacin da ya tafi aiki Karamar Hukumar Alkaleri. Ya ce ba zai tabbatar da cewa mutanensa ne suka yi harbin ko ’yan sara-suka ba, tunda maganar tana gaban ’yan sanda suna bincike kuma har an kama mutanen Garu Security 11.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce sun kama mutum biyu daga cikin wadanda ake tuhuma. Ya kuma ja hankalin ’yan sintiri su guji wuce gona-da-iri, in sun samu wanda suke zargi da laifi kamata ya yi su kai shi ga ’yan sanda in ba za su iya sasantawa ba.