✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma na biyan ’yan bindiga haraji kafin su yi girbi a Zamfara

'Sai kun biya kudin da muka yanka wa garuruwanku sannan za mu bari ku yi noma', injin ’yan bindigar

A Jihar Zamfara, ’yan bindiga sun dawo da kai hare-hare a wasu yankuna a daidai lokacin da manoman ke shirin komawa gonakinsu domin girbe amfanin gonarsu.

Misali a Gundumar Kawaye da ke Karamar Hukumar Anka an dauke manoma da dama lokacin da suka je gonakinsu aiki.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa an yi garkuwa da daruruwan manoma kuma an biya kudade masu yawa don fanso su.

“Daga Gundumar Kawaye, zuwa Sabon Birni da Bawar Daji da Tubiki da sauran yankuna da dama babu manomin da ke iya zuwa gonarsa ya yi aiki.

“A kwanan baya ’yan bindiga sun dauke wadansu manoma shida inda suka ce sai an biya Naira dubu 100 kan kowane mutum.

“Baya ga wannan, girbe amfanin gona ya gagara don sun ce sai an biya haraji za su bari mu yi girbi.

“Sun ce mu hada Naira miliyan daya a kowane kauye kafin su bari mu je gonakin; duk wanda kuwa ya ki biyan wannan zai dandana kudarsu.

“In dai gonar mutum ta kai fiye da kilomita biyar daga garin da yake, to ya manta da batunta, domin da ya je gonar za a dauke shi”, inji shi.

Binciken Aminiya ya gano cewa wata matsalar da manoman jihar ke fuskanta ita ce ta rashin shanun huda saboda galibin shanun an sace su.

“Idan ka ga ana kiwon shanu a wannan daji to mai su yana da alaka ta kusa da wadannan barayi”, inji wata majiya.

A Dansadau, yankin da ya yi suna wajen noma ba a Jihar Zamfara kadai ba har da sassan kasar nan, shi ma ana fuskantar kalubale.

Amma duk da albarkar noma, manoman yankin na fuskantar matsaloli don ba sa iya zuwa gonakinsu.

Wadansu manoma sun shaida wa wakilinmu cewa yawan amfanin gonar da ya kamata a rika diba a yankin ya ragu da fiye da kashi 50 cikin 100.

‘Yadda na tsira’

Wani manomi mai suna Saminu Usman ya shaida wa Aminiya yadda ya tsira daga hanun ’yan bindigar bayan da ya je gona, “Wajen karfe 11 na safe ina aiki a gona a Dansadau, kwatsam sai na ga ’yan bindiga su biyu a kan wani babur sun nufo inda nake.

“Koda na gan su sai jikina ya yi sanyi, don na san abu ne mai sauki su harbe ni. Ina ta kallon su jikina na rawa ina cewa a zuciyata kwanana sun kare. Suna tunkaro ni, har suka iso zuwa gare ni. Sai suka tsaya kowanne dauke da bindiga.

“Na tsaya cikin tsananin fargaba ina jira in ji sun harbe ni, kawai domin abu mafi sauki da za su yi shi ne su dauke ka don kudin fansa.

“Can sai suka ce, kai ba mun hana ku zuwa nan gona ba. Sai daya daga cikinsu ya ce mun fada muku cewa sai kun biya kudin da muka yanka wa garuruwanku sannan za mu bari ku yi noma.

“Ni dai ban ce musu uffan ba, daga nan sai suka hau babur dinsu suka tafi. Saboda firgici sai na dauki kayan aikina na tafi gida. Daga wannan lokaci ban sake zuwa gonar ba”, inji shi.

Wani manomi a yankin mai suna Abubakar Jafaru ya shaida wa wakilinmu cewa yana da gonaki hudu amma ya fi shekara bakwai bai noma su ba.

Malam Abdulhafiz Abdullahi Alkali shi ne Shugaban Kungiyar Manoma ta AFAN ta Zamfara, ya shaida wa wakilinmu cewa wannan matsala tana ci wa manoma tuwo a kwarya.

Kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Dauran bai samu ba, domin bai amsa kiran wakilinmu ba har zuwa lokacin hada wannan rohoto.

Sai dai wani babban jami’in Gwamnatin Jihar Zamfara da ya bukaci a sakaye sunansa ya ce gwamnati na tuntubar masu ruwa-da-tsaki kan sha’anin kuma ana kokarin ganin cewa lamarin bai ta’azzara ba.