Daily Trust Aminiya - ‘Yan bindiga sun hallaka dan jarida a Nasarawa
Subscribe

‘Yan bindiga sun hallaka dan jarida a Nasarawa

‘Yan bindiga sun hallaka tsohon ma’ajin Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa reshen jihar Nasarawa, Mista Benjamin Ekom.

Maharan sun kashe Benjamin wanda kuma tsohon jami’in yada labarai ne na Karamar Hukumar Akun da ke Jihar a daren Litinin a gidansa da ke gundumar Washo.

Kisan nasa na zuwa ne kwanaki bakwai bayan kashe akalla mutum biyar a jihar.

Ko a ranar 27 ga watan Yulin da ya gabata dai sai da aka hallaka mutum biyar, yayin da wasu 14 kuma har yanzu babu duriyarsu a gundumar Dausu ta karamar hukumar Toto.

Dagacin gundumar Aren-Akun, Alhaji Usman Galadima-Umbugadu ya bayyana kashe-kashen a matsayin abin takaici kuma abin Allah-wadai.

Dagacin ya ce Mista Ekom mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen bunkasa yankin, yana mai cewa ilahirin al’ummar sun yi babban rashi.

To sai dai rundunar ‘yan sanda ta jihar ta Nasarawa ta ce har yanzu ba ta samu labarin kisan ba.

Kakakin rundunar, Ramhan Nansel ya ce, “Har yanzu bani da labari amma zan bincika”.

Rahotanni dai sun ce yanzu haka gawar mamacin na can a sashen ajiye gawarwaki na asibitin Akwanga da ke jihar.

texem
More Stories