✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun hallaka shaihin malami na Jami’ar ABU

‘Yan bindiga sun kashe wani shaihin malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ( ABU),  Dokta MB Hassan a lokacin da yake bakin aikinsa a Zamfara.…

‘Yan bindiga sun kashe wani shaihin malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ( ABU),  Dokta MB Hassan a lokacin da yake bakin aikinsa a Zamfara.

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya sanar da mutuwar marigayin a  shafinsa na sada zumunta inda ya bayyana kisan shaihin malamin da abun bakin ciki

” Kaico! Mun yi babban rashi.

“Yanzu nake samun labarin cewa ‘yan bindiga a Zamfara sun kashe Dokta MB Hassan na tsangayar binciken al’amuran noma na Jami’ar ABU a lokacin da yake bakin aiki.

“Allah Ya rahamshe shi, Allah ya kawo mana karshen wannan bala’i.

“Wannan babban rashi ne, kuma da yawa sun rasa ransu a hannun ‘yan bindiga, Allah ya sanya Aljannah ce makomarsa” kamar yadda Solomon Dalung ya rubuta a shafinsa na facebook.

Kafin rasuwar Dokta MB Hassan jami’i ne a Tsangayar Binciken Al’amuran Noma na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.