✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbi ma’aikacin gidan rediyon Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun harbi wani ma’aikacin gidan radiyon tarayya ta Kaduna mai suna Jibril Gwadabe Kuriga a gonarsa da ke kauyansu ta Kuriga Karamar…

Wasu ‘yan bindiga sun harbi wani ma’aikacin gidan radiyon tarayya ta Kaduna mai suna Jibril Gwadabe Kuriga a gonarsa da ke kauyansu ta Kuriga Karamar hukumar Chi‎kun a jiya Talata.

Aminiya ta samu labarin cewa, lamarin ya auku ne da safiyar wannan rana a lokacin da Malam Jibirl da dansa suka je gona domin yin aiki.

Majiyarmu da ke can yankin ta shaidawa Aminiya cewa, an ruga da wanda aka harba a kafa asibiti a Kaduna domin duba lafiyarsa.‎

“Kasan Jibril Gwadabe Kuriga na gidan rediyon Kaduna? Toh an harbe shi a gona yau (Kuriga) inda ya je aiki da yaronsa. Yaron bamu ganshi ba tukunna amma shi mahaifin an wuce da shi Kaduna domin duba lafiyarsa.

“Halin da muke ciki kenan a wannan yanki namu da ke da iyaka da Birnin Gwari domin ko a yau an sake dauke mutane biyu a Udawa. Sun shiga gona sai mutunen suka zo kawai suka dauke su. Har yanzu bamu gamsu ba. ‎Halin da muke ciki a yanzu a wannan yankin kenan.” In ji shi.

‎Wani abokin aikinsa wanda baya san a ambaci sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce, tuni an kai shi wanda aka harba din asibitin sojoji na 44 a Kaduna amma babu likita sai aka wuce da shi asibitin sojojin sama inda ake duba shi.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo, ya ce zai nemi karin bayani daga ofishin ‘yan sandan da ke Buruku kafin ya ce, wani abu amma kuma har ya zuwa lokacin aikawa da labarin nan bai kira wakilinmu ba.