✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun yi garkuwa da mutum 17

Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 17 a masallaci a Nasarawa

Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari wani masallaci tare da yin awon gaba da mutum 17 a kauyen Gwagwada-Sabo da ke gundumar Gadabuke a Jihar Nasarawa.

Daga cikin wadanda aka sace din har da wani ma’aikacin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, mata uku da kuma maza 13.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Usman ya ce lamarin ya faru ne ranar Talata da dare, a lokacin al’ummar yankin na tsaka da yin sallar Isha.

“Maharan sun zo suka fara harbe-harbe ta ko’ina sannan suka yi awon gaba da mutanen zuwa cikin daji”, inji Usman.

Ya ce limamin masallacin da kananan yara ne kawai suka kubuta daga harin.

Iyalan wadanda aka sace din sun ce masu garkuwar sun fara waya da su, suna neman Naira miliyan daya a kan kowane mutum.

“Da farko Naira miliyan 50 suka bukata, amma da muka ci gaba da ba su baki yanzu sun yi sassauci sun ce mu bayar da miliyan daya kan kowane mutum”, inji shi.

Sai dai yunkurinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, ASP Ramhan Nansel ya ci tura saboda bai amsa kira ko rubutaccen sakon da aka tura masa ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.