✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari rugar Fulani a Kaduna

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a rugar Agwala da ke yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna,…

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a rugar Agwala da ke yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suka jikkata wasu tare da banka wa rugar wuta.

Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na Karamar Hukumar Kajuru, Yusuf Musa ya shaida wa manema labarai.

Maharan, kamar yadda Aminiya ta samu labari sun kawo harin ne da tsakar rana, suka yi ta cinna wa gidaje da bukkoki wuta, abin da ya tilastawa mazauna rugar tserewa don tsira da rayukansu.

Yusuf Musa, wanda ya bayyana harin a matsayin wani makirci da neman haddasa fitina tsakanin ‘yan rugar da makwabtansu ‘yan kabilar Adara wadanda suke zaune tare fiye da shekaru 20 ba tare da wata hayaniya ba.

“Don haka wasu ne daga waje suka kawo mana hari,” inji shi.

Sai dai ya ce babu wani asarar rai da aka samu sanadiyyar harin, amma sun yi asarar dukiya mai tarin yawa.

“Da zuwansu kawai sai suka fara sawa gidaje wuta ba tare da cewa komai ba.

Ba na nan a lokacin aka kira ni ta waya aka shaida min abin da yake faruwa bayan sun tafi.” Inji shi

Shi ma shugaban kungiyar MACBAN ta jihar Kaduna, Alhaji Haruna Usman ya tabbatar wa Aminiya ta wayar tarho cew, ya samu rahoton faruwar lamarin duk da cewa babu asarar rai sai dai dukiya da gidajen da aka kona.

Sannan ya yi kira ga ‘yan rugar da su kwantar da hankalinsu tare da jiran gwamnati ta kammala bincikenta don gano marasa son zaman lafiyan da ke neman hautsina kauyen.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya kai ziyarar gani da ido don auna irin asarar da aka tafka a rugar.

Agwala Dutse, wata karamar ruga ce da ke Karamar Hukumar Kajuru wadda Fulani da makiyaya ke zaune a ciki tare da iyalinsu na tsawon lokaci.