✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kai wa dan takarar APC hari a Kwara

Wasu ‘yan bindiga sun kaiwa Mista Raheem Olawuyi dan takarar majalisar wakilai na mazabar kananan hukumomin Irepodun/Ekiti/Oke-Ero da Isin a jihar Kwara, zaben da za…

Wasu ‘yan bindiga sun kaiwa Mista Raheem Olawuyi dan takarar majalisar wakilai na mazabar kananan hukumomin Irepodun/Ekiti/Oke-Ero da Isin a jihar Kwara, zaben da za a yi ranar Asabar 17 ga watan Nuwamba 2018.

Kakakin kamfen na dan takarar Mista Femi David ya bayyana wa wakilin kamfanin dillancin labarai NAN cewa, an kaiwa dan takarar hari ne a yankin Idofin Igbana lokacin da suke gangami a karamar hukumar Oke-Ero.

Dan takarar ya tsallake rijiya da baya ne tare da direbansa da kuma wasu mutum biyu lokacin da suke cikin mota kirar Lexus jeep.