Da Dumi Dumi

’Yan bindiga sun kai wa Sarkin Potiskum hari a Kaduna, sun kashe mutum 6

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i

Wadansu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai wa Sarkin Potiskum da ke Jihar Yobe Alhaji Umaru Bubaram hari a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

’Yan bindigar sun tare titin ne da misalin karfe 9 na dare har zuwa karfe kusan biyu a ranar Talata da ta gabata.

Sarkin na ziyartar wasu sarakuna ne na Arewacin Najeriya domin tattauna shirin kaddamar da Babban Masallacin Juma’a na Potiskum wanda za a bude a ranar 18 ga Janairun nan.

Sarkin na kan hanyarsa ta zuwa Zariya ce cikin daren lokacin da abin ya faru. Sai dai har yanzu babu tabbacin ko shi aka kai wa harin ko kuma tsautsayi ne ya fada masa.

Aminiya ta samu labarin cewa mutum uku daga cikin ayarin Sarkin sun rasu a yayin da ’yan sanda biyu suka samu raunuka.

ADVERTISEMENT

Sarkin Yamma Patiskum Alhaji Gidado Ibrahim wanda ya tabbatar wa wakilinmu aukuwar lamarin, ya ce Sarkin na cikin koshin lafiya.

“Abin babu dadi domin mum rasa mutum uku a cikin ayarinmu sannan wadansu ’yan sanda sun samu rauni amma Sarki na cikin koshin lafiya,” inji shi.

Wakilinmu ya samu shiga inda aka ajiye Sarkin a wani daki a Asibitin Barau Dikko kafin daga bisani a sallame shi, kuma ya tarar da Sarkin a kan gado zaune cikin koshin lafiya amma daga bisani Sarkin ya fito inda aka wuce da shi a cikin motarsa kirar Jeep da misalin karfe 12:24 na rana.

“Allah dai Ya kiyaye sai dai akwai mutanen da suka rasa rayukansu kuma wadansu sun samu raunuka,”  inji shi.

Wadansu daga cikin wadanda suka ga yadda abin ya faru sun shaida wa wakilinmu cewa barayin sun tare titin ne da misalin karfe 9:00 na dare har zuwa kusan karfe biyu na dare.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da ke kusa da inda aka kai harin ya ce, “Muna cikin gida muka rika jin karar bindiga har cikin dare. Da gari ya waye mun ziyarci wurin inda na tarar da motoci ciki har da Jeep. Sannan akwai mutanen da suka samu raunuka wadansu kuma sun rasu,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo ya tabbatar da kai harin da aka yi ga Sarkin na Potiskum.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce akalla mutum shida ne suka rasa rayukansu a yayin wannan hari da aka kai.

Ya ce an kashe mutum hudu daga cikin ayarin Sarkin sannan mutum biyar sun samu rauni. A cewarsa an kai wadanda suka ji rauni Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna. Ya ce wadansu mutane ne da kayan sojoji suka tare titin cikin dare sannan kuma da suka hango ayarin Sarkin Patiskum sai suka bude masa wuta.

Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Umar Muri ya ziyarci Sarkin da sauran wadanda suka samu raunuka a asibitin. Ya kuma bada umurnin a kara yawan ’yan sanda a kan hanyar Zariya zuwa Kaduna

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya