‘Yan bindiga sun kara kashe basarake a Katsina

‘Yan bindiga a jihar Katsina sun kashe Sarkin Fulanin Fafu Alhaji Dikko Usman a cikin tsakar dare.

Maharan sun kai farmaki a garin Mazoji da ke Karamar Hukumar Matazu inda suka bindige Alhaji Dikko wanda shi ne Mai Garin.

Daga bisani maharan sun sulale daga garin ba tare da wata tirjiya daga jami’an tsaro ba.

Dan Marigayin mai suna Fahad ya sanar da aukuwar hakan ta shafinsa na sada zumunta.

Marigayi Alhaji Dikko Usman ma’aikacin lafiya ne kuma a Babban Asibitin da ke garin Kankia.

Kashe Mai Garin na Fafu na zuwa ne kasa da mako biyu da ‘yan bindiga suka kashe wani hakimi a jihar.

Wadancan maharan sun harbe Hakimin Yantumaki a Karamar Hukumar Danmusa.

Marigayi Alhaji Atiku Maidabino ya rasu ne bayan ‘yan bindiga sun bude masa wuta a gidansa da talatainin dare.

Har yanzu dai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ba ta yi tsokaci kan harin ba tukuna.