Da Dumi Dumi

’Yan bindiga sun kashe DPO da mai ciki a Edo

Yan sanda

Wadansu ’yan bindiga sun lallava zuwa ofishin ’yan sanda da ke Afuze, hedkwatar Karamar Hukumar Owan ta Gabas da ke Jihar Edo a makon jiya, suka kai hari suka kashe babbar jami’ar ofishin (DPO) tare da wadansu mutum hudu.

Hedkwatar Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo ta bayar da sunayen wadanda harin ya shafa da suka hada da  DPO, Tosimani Ojo da Sufeto Sado Isaac. Sauran sun hada da wata ’yar sanda mai mukamin Sajen, wacce ke dauke da tsohon ciki, mai suna Justina Aghomon da kuma Kofur Glory David.

Aminiya ta samu labari daga wata majiya ta kusa da ofishin ’yan sanda na Afuze, cewa ’yan bindigar da suke je ofishin sun yaudari DPO din, wacce a lokacin take gidanta, suka ce ta zo ofis ta yi baki. Ita kuma ta baro gidanta ta zo domin ta gana da bakin nata. Majiyar ta ce bayan da jami’ar ta zo ofishin sai suka yi amfani da wani abu mai fashewa mai karfin gaske, suka jefa mata, daga bisani kuma suka far wa ragowar ’yan sandan da ke bakin aiki a ofishin. Cikinsu har da Aghomon, wadda kadddara ta dawo da ita ofishin na Afuze, bayan da aka yi mata sauyin wurin aiki watannin baya zuwa wani wuri.

Kwamishinan ’Yan sandan  Jihar Edo, Muhammad Danmalam ya bayyana cewa ba za a bar abin haka ba sai an yi bincike an kamo wadanda suka aikata wannan ta’addanci.

Kwamishinan, wanda ya ziyarci ofishin ya nuna matukar vacin rai da takaicinsa game da lamarin kuma ya jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya