Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan bindiga sun kashe hakimin Balle a Sakkwato

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kashe Hakimin garin Balle, Alhaji Ibrahim Aliyu, mai shekaru 82 a duniya.

Garin Balle, hedkwatar karamar hukumar Gudu a jihar Sakkwato, ya kasance garin da ake zaman lafiya, kafin wannan harin da ‘yan bindigar suka kaddamar a jiya Talata.

ADVERTISEMENT

Ganau sunce, ‘yan bindigar da suka yi wa garin dirar mikiya a maraicen Talata kan babura shida, sun bankawa ofishin ‘yan sanda wuta tare da wasu motocin sintirin jami’an tsaro da ma wasu ababen hawa na jama’a.

Sun kuma kashe wani jami’in dan sanda, wanda ba a tantance ba, a wata unguwa mai suna, Karfen Sarkin.

ADVERTISEMENT

Wani jami’in asibiti, ya shaidawa wakilinmu, cewar, ‘yan bindigar sun kutsa ta shingen da ya kewaye gidan hakimin, suka fitar dashi waje  kana suka harbe shi.

Dan majalisa mai wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Sakkwato, Alhaji Faruk Balle, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bukaci gwamnati da ta yi wani abu akai dan kare rayukan al’umma.