✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe Hakimin ‘Yantumaki

‘Yan bindiga sun halaka Hakimin ‘Yantumaki, Sarkin Fulanin Dangin Katsina. Da talatainin daren jiya ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari…

‘Yan bindiga sun halaka Hakimin ‘Yantumaki, Sarkin Fulanin Dangin Katsina.

Da talatainin daren jiya ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari garin ‘Yantumaki da ke Karamar Hukumar Danmusa cikin Jihar Katsina.

Maharan sun kashe hakimin garin Alhaji Abu Atiku Maidabino bayan da suka iske shi har cikin gidansa sannan suka bude masa wuta.

‘Yan bindiga sun kashe jama’a a kauyukan Katsina

Yadda ‘yan bindiga suka kone mutum 30 a Katsina

Rahotanni sun nuna ‘yan bindigar sun zo da yawa kuma gidan hakimin kawai suka kai harin.

Karamar Hukumar Danmusa dai na daya daga cikin kananan hukumomin da matsalar hare-haren ‘yan bindiga ya yi kamari a jihar Katsina.