Da Dumi Dumi

‘Yan bindiga sun kashe jami’an JTF 6 da tarwatsa mutum 98 a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Shinkafi  da ke jihar Zamfara, sun kashe jami’an tsaron farin kaya na JTF shida . Mataimakin shugaban karamar hukumar Alhaji Sani Galadima, ne ya sanar da hakan a jiya Litinin lokacin da Ministan ma’aikatan cikin gida na Najeriya Abdulrahaman Dambazau ya ziyarci jihar.

Ministan ya ziyarci jihar ne da nufin magance kalubalen tsaron da yake fuskantar jihar. An kashe jami’an tsaron a hanyar komawa kauyen da suke, bayan sun karbi albashin su.

Alhaji Sani, ya ce a ranar Lahadi ne ‘yan bindigar suka aikawa da hakimin lardin Shinkafi cewa, su na nan zuwa garin Shinkahfi don kaddamar da hari.

Share