Aminiya

’Yan bindiga sun kashe jariri da sace jami’in KASTELEA a Kaduna

Wasu da ake zaton ‘yan ta’addan Birnin Gwari ne sun harbe wani jariri, sannan suka sace wani ma’aikacin kula da ababen hawa  watau KASTELEA akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a jihar.‎

Ma’aikacin KASTELEA din mai Suna Hamza, an ce yana kan hanyarsa ce ta komawa gida a Birnin Gwari inda iyalansa suke domin yin hoton karshen mako.

ADVERTISEMENT

Kuma lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar makon jiya lokacin da ‘yan ta’addan suka budewa motar wuta da suke ciki sannan suka sace shi.

Wani dan sintiri da ke yankin wanda kuma bai ambaci sunansa ba saboda tsaro ya tabbatarwa da Aminiya cewa motoci biyu aka kai wa hari a ranar Juma’ar kuma daya daga cikin direbobin motar ya rasa ransa.

ADVERTISEMENT

“Eh, motoci biyu aka kaiwa hari a ranar Juma’ar a wani wuri da ake kira Gaban Gayan mai nisan kilomita kadan daga Kurega akan titin Kaduna zuwa Birnin Gwari. Yan’ta’addan sun budewa motocin wuta ne inda harsashi ya samu dan jaririn da ke hannun mahaifiyarsa da ke cikin daya motar.

“A nan ta ke mutum daya ya rasu sannan wanda muke tsammanin direban motar ne. Sannan mutum biyu sun samu raunuka‎ an kuma kwashe su zuwa wani asibiti da ke Kaduna. An yi jana’zar jaririn domin shi da mahaifiyarsa ‘yan wani kauye ne da ke kusa da Kurega, ” in ji shi.

A cewarsa, mahaifiyar yaron itama ta dan samu rauni amma sai dai babu cikekken bayani akan ko suna cikin motar da aka sace ma’aikacin KASTELEA a lokacin wannan hari da aka kai masu.

Aminiya ta gana da wani dan KASTELEA a jihar wanda ya boye sunansa amma ya tabbatar da sace abokin aikin nasu.

Ya ce, ‎ sun sace shi ne akan hanyarsa na zuwa hotun karshen mako a gida kuma sun kira cewa suna bukatar kudin famsa. Ya bayyanawa abokin aikin nasu a matsayin mutumin kirki.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Yakubu Sabo, ya ce zai kira wakilinmu idan ya samu bayanin abin da ya faru amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin aikawa da rahoton.