✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe Mai Unguwa a Filato

Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko suwaye ba sun kai hari fadar Mai Unguwar garin Kaduni Muhammad Bayero, da ke gundumar Langai a…

Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko suwaye ba sun kai hari fadar Mai Unguwar garin Kaduni Muhammad Bayero, da ke gundumar Langai a Karamar Hukumar Mangu ta jihar Filato a daren jiya Lahadi.

Mai Unguwar wanda rawanin Rit Kadunu, ‘yan bindigar sun harbe shi ne da misalin karfe 8:10 na dare yayin wani da yake zaune a fadar aka yi kuskuren harbinsa a kafa.

A yayin da tsohon Kwamishinan harkokin kasuwanci da masana’antu na jihar Honorabul Yakubu Idi Usman, yake bayyana takaicinsa ga manema labarai ya ce an yi jana’izar Mai Unguwar a safiyar yau Litinin kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.