✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

`Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Benuwe

Rahotanni na bayyana cewa, wasu `yan bindiga sun kashe mutum 10 a wani sabon hari da suka kai a unguwar Tser Uoreleegeb a shiyyar Ubabai…

Rahotanni na bayyana cewa, wasu `yan bindiga sun kashe mutum 10 a wani sabon hari da suka kai a unguwar Tser Uoreleegeb a shiyyar Ubabai da ke karamar hukumar Guma jihar Benuwe.

Majiyarmu ta gano cewa, lamarin ya faru ne a daren ranar Talata lokacin da wadanda aka kashe ke barci a waje, sai `yan bindigar suka yi ta harbin su bayan sun kashe nan take suka tsere daga unguwar.

Shugaban karamar hukumar Guma Richard Shior ya tabbatar da kisan mutanen da `yan bindigan suka yi.