✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 14 a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 14 a kauyen Karaye da ke gundumar Gwalli a Karamar Hukumar Gummi ta jihar Zamfara. Wasu mazauna kauyen sun…

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 14 a kauyen Karaye da ke gundumar Gwalli a Karamar Hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Wasu mazauna kauyen sun bayyanawa majiyarmu cewa, ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne da muggan makamai akan babura da misalin karfe 9 na dare, inda suka fara harbin jama’ar garin. Sun kone gidajen jama’a da  shaguna da kuma kayan abincin jama’ar unguwar.

Wani mazaunin unguwar mai suna Mustapha Aminu, ya sanarwa Aminiya cewa, ‘yan bindigar sun fara shiga kauyen Kurfa da ke gundumar, anan suka kwace baburan jama’a da fasa shagunansu.