Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 17 a kauyuka uku da suke karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara. Mazauna garin sun ce, ‘yan bindigar su kai harin ne akan babura inda suka fara shiga garin Gidan Kaso ranar Asabar suka kashe mutum bakwai.
Wani mazaunin garin mai suna Tukur Yusuf, ya ce bayan ‘yan bindigar sun kashe mutanen sun hana jama’ar garin daukar gawarwakin don birne su, har sai da jami’an tsaro da ‘yan banga suka shiga garin kafin a kwashe gawarwakin.
A jiya Lahadi ‘yan bindigar sun kai hari unguwar Dan Dambo inda suka kashe mutum hudu da kwashe dabbobin jama’ar garin.