✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Kaduna

Mutum biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hari mai kama da ramuwar gayya da wadansu ’yan bindiga suka kai a kauyen Tsonje da…

Mutum biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hari mai kama da ramuwar gayya da wadansu ’yan bindiga suka kai a kauyen Tsonje da kan hanyar Kagoro zuwa Gidan Waya a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna ranar Alhamis din makon jiya.

Mutanen masu suna, Kasang Ambakadi da Clement Moses manoma ne da ake tunanin ’yan bindigar sun yi musu kwanton bauna a gonakinsu suka hallaka su.

Idan za a iya tunawa Aminiya ta ruwaito labarin kashe wani manomin bammi da wadansu da ake zargi da satar shanu suka yi a kauyen na Tsonje, abin da ya harzuka kabilun wurin suka kai harin da suka kashe makiyaya uku da shanu biyu.

Wani ganau a yankin ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya yi matukar tayar da hankalin mutanen yankin abin da ya kai ga manoma kaurace wa gonakinsu na wani lokaci a makon.

Yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukumar Kaura, Misis Joy Aku ta ce an kai gawarwakin mutanen biyu zuwa Babban Asibitin Kaura, sannan ta yi kira ga mutanen yankin su guji daukar doka a hannunsu idan wani abu ya faru don gudun hare-haren daukar fansa da kan biyo baya.

Ta ce tuni jami’an tsaro a yankin suka yi nasarar kwantar da duk wata tarzoma da ka iya tasowa sanadiyyar kisan mutanen biyu.