✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

`Yan bindiga sun kashe mutum 2 a kauyen Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu a kauyen Ambe Madaki a lardin Gwantu na karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna. Wadanda suka kashe su…

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu a kauyen Ambe Madaki a lardin Gwantu na karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.

Wadanda suka kashe su ne Ibrahim Manzo mai shekara 70 da dan uwansa Barnabas Musa mai shekara 45.

Shugaban karamar hukumar Sanga Mista Charles Danladi, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya yi Allah wadai da harin ‘yan bindigar.