✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Katsina

A daren ranar Talata wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina. Kauyukan da aka…

A daren ranar Talata wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Kauyukan da aka kai harin sun hada da: Dan Marke Z, da Dan Sabau da Karya wadanfda suka hada iyaka da jihar Zamfara.
Shugaban riko na karamar hukumar Anas Isa ya tabbatar da kisan gillar da aka yi wa jama’an kauyukan, ya kuma ce, ‘yan bindiga sun budewa jama’ar kauyen wuta ne daga bisani suka kashe masu dabbobin su.