Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

`Yan bindiga sun kashe mutum 22 a Birnin Gwari

Rahotanni na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun afkawa unguwar Layin Maigwari da ke karamar hukumar Birnin Gwari  a jihar Kaduna inda suka kashe mutum 22.

A cewar rahoton ‘yan bindiga sun shiga unguwar ne da misalin karfe 7 na dare inda suka dinga budewa jama’ar garin wuta.

ADVERTISEMENT

Majiyarmu ta gano cewa, ‘yan bindigar sun ta harbin jama’a na kusan sa’a daya, wanda hakan ya haddasa kisan mutum 22 da raunata wasu da dama agarin.

ADVERTISEMENT