✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yan bindiga sun kashe mutum 25 a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutum 25 a wani hari da suka kai wasu kauyuka a Kananan Hukumomin Talata Mafara da Maru a jihar Zamfara.…

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutum 25 a wani hari da suka kai wasu kauyuka a Kananan Hukumomin Talata Mafara da Maru a jihar Zamfara.

Mazauna kauyukan da lamarin ya faru su shaida wa Aminiya cewa lamarin ya fara ne bayan ‘yan bindigar sun isa kauyen Awala a ranar Laraba inda suka yi yunkurin satar shanu.

Sai dai mazauna garin sun ki barin ‘yan ta’addan tafiya da dabbobin, har suka yi nasarar kashe da dama daga cikinsu.

Hakan ta sa maharan sake dawowa bayan kwana daya a kan a babura suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi a kauyukan Zaman Gira, Awala, Bolakke, Yargada da kuma Gidan Runji.

Maharan sun sake komawa garin na Zaman Gira inda suka far wa mutanen da ke kokarin jana’izar wadanda suka rasu a harin farkon a wata makabarta, har suka halaka mutane da dama.

To sai dai Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya shaida wa Aminiya cewa nan gaba kadan Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar zai yi wa yan jarida jawabi a kan lamarin .