✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 da yin garkuwa da 6 a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Shinkafi jihar Zamfara a daren ranar Alhamis sun yi garkuwa  da mutum 6 ciki harda wasu mutumu…

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Shinkafi jihar Zamfara a daren ranar Alhamis sun yi garkuwa  da mutum 6 ciki harda wasu mutumu biyu ‘yan kasar Ghana.

Majiyarmu ta samu rahoton yau Lahadi cewa, ‘yan bindigar sun shiga wani gida da ke makwabtaka da wani gida da ake kira gidan Alhaji Mai Akuya, wadanda aka yi garkuwan da su dai masu sana’ar sayar da albasa ne a kasuwar Shinkafi.

Daya daga cikin ‘yan Ghanan da aka yi garkuwa da shi ya tsere amma sauran na hannun masu garkuwan. Wani mazaunin unguwar Aliyu Usman ya bayyana wa majiyarmu cewa, kafin ‘yan bindigar su yi garkuwa da mutanen sun dakatar da wata tirela da ta taso daga kasuwar Shinkafi suka kashe mutum uku daga cikin motar.