Search
Subscribe
‘Yan bindiga sun kashe mutum 33 a cikin mako 1 – Matasan Batsari

‘Yan bindiga sun kashe mutum 33 a cikin mako 1 – Matasan Batsari

Matasan karamar hukumar Batsari a jihar Katsina sun ce, `yan bindiga da suka addabi garin sun kashe mutum 14 a hanyar Batsari zuwa Safana da ke jihar ranar Litinin, yayin da suka kashe mutum 19 a cikin makon nan duk a a cikin garin.

Matasan sun bukaci a sako wasu ‘yan banga da jami’an ‘yan sanda suka tsare saboda ya kashe wani dam bindiga a yankin. Matasan sun yi kiran ne a karkashin kungiyar matasan Batsari  kuma sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin su game ci gaba da kisan gillar da ake yi a unguwanni da kauyukan garin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin