✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 34 a kauyuka 3 na Zamfara

Wasu ’yan bindiga sun kashe kimanin mutum 35 a wani sabon hari da suka kai kauyuka uku a Karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.…

Wasu ’yan bindiga sun kashe kimanin mutum 35 a wani sabon hari da suka kai kauyuka uku a Karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.

‘Yan bindigar sun shiga kauyukan da suka hada da: Kwallido da Tungar Kahau da kuma Gidan Wawa akan babura mai kafa uku. Kauyukan sun kai nisan Killomita 20 zuwa birnin Shinkafi.

Wani mazaunin garin mai suna Sani Aliyu, ya bayyanawa Wakilinmu cewa, ‘yan bindigar sun kaiwa wadanda suka kashe harin a gonakin su yayin da wasu kuma suka kai masu hari a gidajensu inda suka yi ta harbin su.

Maharan sun kashe mutum 12 a kauyen Gidan Wawa, sun kashe mutum 22 Tungar Kahau da kuma kashe mutum 1 Kwallido.