✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da yin garkuwa da 6 a Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun sake kashe mutum 7 tare da yin garkuwa da mutum 6 a kauyuka 10 da ke Karamar Hukumar Kankara ta jihar…

Wasu ‘yan bindiga sun sake kashe mutum 7 tare da yin garkuwa da mutum 6 a kauyuka 10 da ke Karamar Hukumar Kankara ta jihar Katsina duk a ranar Asabar.

Kauyukan da aka kai harin sun hada da: Pawwa, Katoge, Korawa, Dan Hayi, Gidan Mai Godiya, Gidan Dan Maarbi, da `Yar Kuka.

Maharan su kuma kone gidaje da shaguna da dama a wannan harin wanda ya faru da misalin karfe 5 na yamma zuwa 7 na yamma. A harin dai an yi garkuwa da mata uku da yara uku.

Wannan harin ya yi sanadiyyar fusata wasu matasa ranar Lahadi, inda suka yi zanga-zanga tare da rufe manyan hanyoyin wucewa zuwa jihohin Sakkwato, Kano da shiga cikin garin Katsina.