Da Dumi Dumi

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 10 a Jos

Ana zaman dardar a unguwar Rukuba kusa da hanyar Jos babban birnin Filato bayan da aka kai wani kazamin hari daren jiya Alhamis.

Har zuwa safiyar yau Juma’a jama’ar yankin na cikin dardar sakamakon harin da ‘yan bindigar suka kai wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da mutum 10.

Matasan yankin sun fusata inda suke ta binciken masu motoci.

Jami’in watsa labarai na rundanar sojojin Operation Safe Haven Manjo Adam Umar da jami’in hulda jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar DSP Tyopev Terna sun ce, a yanzu haka an girke jami’an tsaro a yankin.

ADVERTISEMENT
Share