✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan kasuwa 3 akan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna 

Wasu da ake zargin yan ta’addan Birnin Gwari ne sun harbe wasu ‘yan kasuwa uku a akan hanyar Birin Gwari zuwa Kaduna a Ranar Lahadi…

Wasu da ake zargin yan ta’addan Birnin Gwari ne sun harbe wasu ‘yan kasuwa uku a akan hanyar Birin Gwari zuwa Kaduna a Ranar Lahadi nan data wuce.

Aminiya ta samu labarin cewa, ‘yan Kasuwar na kan hanyar dawo wa ne daga yankin garin Udawa da yammancin jiya Lahadi lokacin da ‘yan bindigan suka budewa motarsu wuta.

Daya daga cikin shugabannin ‘yan sakai da ke Yankin Udawa wanda bai san a ambaci sunansa ne ya sanarwa da wakilin mu yadda lamarin ya auku.

“Abin babu dadi ko kadan domin ‘yan kasuwar sun baro kasuwar udawa ce a lokacin da labari ya iso cewa, wai ‘yan ta’addan zasu kawo hari cikin kasuwa sai jama’a da wasu ‘yan kasuwa suka rika gudu wanda hakan ya janyo hasarar dukiya mai yawa.

“Ana cikin wannan rudani ne sai ‘yan kasuwar da suka zo cin kasuwa daga Kaduna suka shiga mota da nufin komawa gida. To akan  hanyarsu  ne sai yan ta’addan suka budewa motar da suke ciki wuta wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwar mutanen,” in ji shi.