Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
’Yan bindiga sun kashe ’yan kasuwa 7 a Kaduna

’Yan bindiga sun kashe ’yan kasuwa 7 a Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun kai wani hari a kasuwar kauyen da ke garin Maro a masarautar Adara a karamar Kajuru, inda suka harbe mutum bakwai.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba da misalin karfe 7:30 lokacin da ’yan kasuwar ke shirin tafiya gidajensu.

A cewar wata majiya da ke kusa da Hakimin Kufana ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ’yan bindigan basu dauki komai a wajen ’yan kasuwar ba.

“Babu abin da suka dauka ko karba a wajen ’yan kasuwar. Zuwa kurum suka yi suka budewa wasu daga cikin ’yan Kasuwar wuta inda aka shaida mana cewa, yanzu hakan an kashe mutum bakwai. Hakimi na shirin zuwa wurin kenan a yanzu domin ganewa idanunsa.” In ji shi.

Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar ASP Muhammad Jalige, wanda ya ce zai bincika ya samu bayanin kafin ya ce wani abu.