Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan bindiga sun kashe ‘Yan sanda biyu a Bayelsa

Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu da ke gadin otel din Odeme,da ke hanyar Alamesiagha a Yenaguwa babban birnin jihar Bayelsa bayan sun shiga otel din a daren Asabar.

Otel din mallakin Sanata Emmanuel Paulker ne mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya a majalisar dattawa.

ADVERTISEMENT

Wani da yaga aukuwar lamarin ya ce, ‘yan bindigan sun yi ta harbi ne na tsawan mintuna 30 kafin su yi awan gaba da bindigogin ‘yan sandan.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar DSP Asinim Butswat ya ce, jami’an na binciken lamarin.

ADVERTISEMENT