✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

Yan bindiga sun sace dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Lame a karamar Hukumar Toro, Alhaji Yusuf C. Nuhu na Jam’iyyar APC a…

Yan bindiga sun sace dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Lame a karamar Hukumar Toro, Alhaji Yusuf C. Nuhu na Jam’iyyar APC a ranar Litinin kwana daya da sace wani ma’aikacin allurar rigakafin cutar shan inna a karamar Hukumar Darazo da ke jihar mai suna Ali Garba.
An sace dan majalisa Yusuf Nuhu ne a garinsu Zalau bayan ya yi Sallar Magariba a masallacin kofar gidansa da ke garin, kuma yana fara nafila, sai biyu daga cikin ’yan bindigar da aka yi Sallah da su suka fito da bindiga suka yi garkuwa da dan majalisar suka fita suka sanya shi cikin mota kirar Gulf 3 suka ci gaba da harba bindigogi suka gudu da shi.
Wani wanda aka yi abin kan idonsa mai suna Nuhu Haro Abubakar ya bayyana wa wakilinmu cewa mutanen garin suka hau motoci da babura suka bi sawun ’yan bindigar, kuma da suka ga fitillun ababen hawa na biyo su, sai suka tsaya da motarsu suka kashe wuta. Ya ce su ma da suke bin su sai suka tsaya daga nesa ana shawarar irin isar da za a yi gare su, “Ashe sun fita daga cikin motar sun shiga daji da shi, daga bisani aka samu wadanda suka yi kundumbala suka isa wurin motar sai suka iske ba kowa ciki, kuma an mika wa jami’an tsaro motar,”inji shi.
Nuhu Haro ya ce har zuwa ranar Talata jama’a na ta yawo domin nemo farautar maharan a dajin Rahama da Rishi da Ashura da sauransu amma babu labarinsu.
Matar dan majalisar, Suwaiba Yusuf ta ce bayan mijinta ya yi alwala sai ya fita zuwa masallaci kuma bayan idar da Sallah ne sai suka ji harbe-harbe suka ga ’yan bindiga a kofar gidan sun kange ko’ina. Ta ce daga baya ne ta ji an ce mijnta, “Don haka ina rokion jama’a su taimaka mana da addu’ar Allah Ya sa a sako shi,” inji ta.
Shugaban Majalisar Jihar Bauchi Alhaji Yahaya Mohammed Miya ya bayyana alhininsa game da wannan abu, ya ce sun yi zaman gaggawa kuma suna hada kai da jami’an tsaro domin tsananta bincike a cikin dazuka don a kubuto da abokin aikin nasu.
A ranar Lahadin da ta gabata ’yan bindiga sun sace jami’an allurar rigakafi uku a garin Dayi da da ka karamar Hukumar Darazo, sai dai sun sako biyu daga cikinsu yayin da suke rike da wani mai suna Ali Garba.
An jima ana zargin ana ganin ’yan bindiga suna atisaye tun kimanin wata guda a cikin dazukan Soro zuwa Darazo. Wani mazaunin yankin ya bayyana wa Aminiya cewa wasu lokuta har jirgi mai saukar ungulu na sauka cikin dajin. Kuma ana ganin manyan motoci na shiga da fita amma sun yi ruhoto har yanzu ba wani mataki da aka dauka.
Mako biyu da suka wuce an sace tsohon dan Majalisar Wakilai Alhaji Samaila Ilali a Darazo kuma rahotannin da ba na gwamnati ba sun ce iyalansa sun biya diyyar Naira milyian goma kafin a sako shi.
Kakaki rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ASP Haruna Mohammed ya tabbatar da sace Yusuf Nuhu da ma’aikacin allurar rigakafin kuma ya ce suna ci gaba da biincike domin kubutar da su.