✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mai jego da mutum 5 a Kaduna

A daren yau Laraban nan ne wasu ‘yan bindiga suka sace wata mai jego da wasu mutum 5 a Unguwar Dan Mani da ke a…

A daren yau Laraban nan ne wasu ‘yan bindiga suka sace wata mai jego da wasu mutum 5 a Unguwar Dan Mani da ke a Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna.

‘Yan bindigan sun yi wa unguwar dirar mikiya ne da misalin karfe 3:15 na dare inda suka rika bi gidagida suna daukar mutanen.

Daya daga cikin masu unguwannin yankin wanda bai so a ambaci sunansa ba ya tabba‎tarwa da Aminiya aukuwar lamarin inda ya ce, sace mutanen ya jefa tsoro a zukatar jama’a.

“Lamarin ya auku ne da misalin karfe 3:15 na dare sai muka rika jin harbi kusan dukkanmu da ke unguwar nan bamu yi barci ba. Yanzu haka sun sace wata mata mai suna matar Gali wacce mai jego ce, shi mijin nata Gali ya tsira. Sun sace Gambo mai Tais da Bukar Mandara. Akalla dai mutum shida muka tabbatar da an dauka,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta kawo masu dauki domin a cewarsa wannan ne karo na farko da masu garkuwa da mutane suka yi nasarar daukar mutane a unguwar.