Da Dumi Dumi

’Yan bindiga sun sace mutum 16 a Birnin Gwari

Masu garkuwa da mutane dauke da makamai sun sace mutum 16 a karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna. Lamarin ya auku ne a dajin Falwaya da ke kusa da garin Bagoma a yankin Birnin Gwari a shekaranjiya Laraba.

Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya ce wadanda aka sace duk ’yan gari daya ne kuma suna kan hanyarsu ce ta komawa gida ne bayan sun fito daga wurin sana’arsu ta hakar ma’adinai.

Ya ce tuni hukumarsu ta aika da jami’anta domin su taimaka wajen ceto wadanda aka sace daga hannun masu garkuwa da su. “Wadanda aka sace, mun samu labarin cewa suna cikin mota ce roka, a hanyarsu ta komawa gida bayan sun dawo daga wajen  hakar ma’adinai suke yi, sai wadansu suka tsayar da su suka kwashe su. Daga cikin wadanda aka sace akwai wani mai suna Isa Tanimu da  mutum goma sha biyar. Jami’anmu sun fara kokarin gano inda suke saboda wadanda ake garkuwa da su sun riga sun fara magana tare da neman a ba su kudin fansa,” inji shi.

“Wannan abin damuwa ne amma muna kokarin  kubutar da su daga hannun bata-garin sannan kuma mu kama masu garkuwan da su domin a hukunta su,” inji shi.

Ya nemi jama’ar gari su ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.

ADVERTISEMENT

A makon jiya ne wani dan jarida da matarsa da kannensa biyu suka samu kubuta bayan sace su a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da aka yi. An sake su ne bayan sun kwashe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutanen kuma sai da suka biya kudin fansa.

Binciken Aminiya ya gano cewa satar mutane na ci gaba da faruwa a wasu sassa na Jihar Kaduna, musamman a yankinBirnin Gwari da kuma dajin Rigasa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya