Aminiya

’Yan bindiga sun sake yin garkuwa da mutum 2 a Abuja

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da mutum biyu a garin Abaji da ke cikin babban birnin tarayya Abuja.

Wadanda aka yi garkuwan da su sun hada da: Murtala Maji Nasara da Yusuf Ibrahim, an yi garkuwan da su ne a tsakar daren yau Alhamis da misalin karfe 1:09 lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari cikin garin.

ADVERTISEMENT

Wani makwabcin gidan da aka kai harin mai suna Yahaya, ya ce ‘yan bindigar sun shiga cikin garin ne dauke da miyagun makamai sannan suka fara shiga cikin gidan wani mutum mai suna Murtala.

Sun kewaye gidan rike da bindigogi sannan wasu suka shiga cikin gidan, daga nan suka wuce da wadanda suke nema.

ADVERTISEMENT