Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan bindiga sun shirya mika wuya a Zamfara- Kwamishina

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Usman Nagoggo, ya ce ‘yan bindigar da suka addabi jihar sun shirya tsaf don mika wuya da aje makamansu da nufin tabbatar da samun zaman lafiya a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana hakan ne yau a wata ganawa da suka yi da ‘yan bangar jihar wanda aka fi sani da ‘Yan Sakai. Ya bayyana cewa, hukumomi sun tattaunawa da ‘yan bindigar game da dakatar hare-haren da suke kaiwa a jihar ta hanyar bin sharuddan su.

ADVERTISEMENT

‘Yan bindigar jihar dai sun dade suna yi jama’ar jihar kisan gilla a yankunan jihar musamman kasuwanni kauye da sauran wurare.

ADVERTISEMENT