Search
Subscribe
’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al’ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka tarwatsa kauyuka 16 tare da halaka ’yan banga uku a yankin.

Aminiya ta samu bayanin cewa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi lokacin da ’yan bindigan suka shigo cikin garuruwan da ke Igabi ta Yamma suka bukaci mazauna yankin su bar wurin ko su halaka su.

Bayanai sun nuna cewa, wasu ’yan sintiri ko ’yan banga a yankin ne suka shiga dajin da nufin tarwatsa ’yan bindigan wadanda suka dade suna cutar da su a yankin wanda sakamakon hakan ne ’yan banga uku suka halaka.

Wakilinmu wanda ya ziyarci sansanin da mutanen ke zaune ya ruwaito cewa, mata da yara kana kusan dubu 1200 ne suka nemi mafaka a makarantar Firemare ta Birnin Yero.

Mai Unguwar Gide Jibril Abdullahi, ya  bayyana sunayen kauyukan da aka tarwatsa kamar haka Dura da unguwar Gide da unguwar Dan Gauta da unguwar Nayawo da unguwar Makeri da kigani da Sabon Gida da Dallatu da Anguwar Ahmadu da Sabon Gari.‎

Sauran sun hada da Kusau da gidan Sarkin Noma da unguwar Pati da unguwar Amfani da unguwar Tofa sa soran Giwa.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan Sandan Jihar Yakubu Sabo, abin ya ci tura domin bai amsa wayarsa ba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin